Bayan Hana Su Taro, 'Yan Tinubu Must Sun Yi wa 'Yan Sanda Tambaya 9 Masu Zafi
- Abba Hikima ya buƙaci rundunar ’yan sandan jihar Kano ta bayyana dalilin hana gudanar da taron ƙungiyar Tinubu Must Go a Kano
- Lauyan ya ba rundunar wa’adin kwana bakwai domin amsa tambaya tara da ya gabatar bisa dokar ’yancin samun bayanai ta shekarar 2011.
- Ya yi gargaɗin cewa ƙin bayar da bayanan da doka ta tanada na iya zama laifi, yana mai cewa babu wani jami’in gwamnati da ya fi ƙarfin doka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Jagoran Tinubu Must Go, Hikima ya buƙaci rundunar ’yan sandan jihar Kano ta yi bayani kan dalilin hana gudanar da taron su a wani wuri da aka kama haya, duk da ikirarin rundunar cewa taron ya halatta kuma ba ya buƙatar izinin ’yan sanda.
Abba Hikima ya ce ya aika wa rundunar tambayoyi tara bisa dokar ’yancin samun bayanai ta shekarar 2011, inda ya buƙaci a ba shi amsoshi cikin kwana bakwai da karɓar wasiƙar.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, ya yi gargaɗin cewa sashe na 7(4) da 7(5) na dokar sun tanadi matakan da za a ɗauka idan aka ƙi bayar da bayanan da aka nema ba bisa ƙa'ida ba.
Tambaya 9 aka yi wa ’yan sanda
A cikin wasiƙar, Abba Hikima ya gabatar da tambaya tara da ya ce suna da muhimmanci wajen fahimtar matakin da rundunar ’yan sanda ta ɗauka kan taron.
Ga tambayoyin da ya buƙaci rundunar ta amsa:
1. Mene ne ainihin dalili da hujjar hana taron TMG? Ya buƙaci rundunar ta bayyana dalilin hana gudanar da taron a wurin da aka kama haya.
2. Wane irin barazana ce ’yan sanda suka ce suna kare masu taron daga gare ta? Ya nemi ƙarin bayani kan irin barazanar da rundunar ta ce tana ƙoƙarin hana faruwarta.
3. Su waye suka yi barazanar kawo cikas ga taron, kuma wane mataki aka ɗauka a kansu? Ya tambayi dalilin da ya sa ’yan sanda suka ɗauki mataki kan waɗanda aka yi wa barazanar maimakon waɗanda ake zargin za su kawo cikas.
4. Me ya sa rundunar ta kasa tabbatar da tsaron wurin taron duk da tura jami’an tsaro masu ɗauke da makamai? Ya nemi sanin dalilin da ya sa ba a tabbatar da tsaro domin a gudanar da taron cikin lumana ba.
5. Ta yaya hana mahalarta shiga wurin taro mai tsaro, tare da barin su a kan tituna, zai zama kariya gare su? Ya nemi rundunar ta yi bayanin yadda matakin ya dace da ikirarin kare rayukan mahalarta.
6. Me ya sa aka harba hayaki mai sa hawaye kan wasu mahalarta taron da rundunar ta ce ta zo domin kare su? Ya nemi bayani kan dalilin amfani da hayakin kan mutanen da aka ce ana karewa.
7. Shin hana taron yana da alaƙa da wata umarni ko manufar dakile ayyukan siyasa na lumana da mutanen da ke adawa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa? Ya buƙaci rundunar ta fayyace ko akwai wani umarni ko haɗin gwiwa da ya jawo matakin.
8. Shin rundunar ’yan sandan Kano ce kaɗai ta yanke shawarar hana taron, ko kuma wani ɓangare ne ya bayar da umarnin ko ya shiga cikin matakin? Ya nemi sanin inda shawarar ta samo asali.
9. Shin rundunar ta amince da haƙƙin ’yan ƙasa na ci gaba da gudanar da tarukan TMG na lumana, kuma a shirye take ta kare su maimakon hana su? Ya nemi tabbacin cewa za a bar masu taron su gudanar da ayyukansu na halal a nan gaba.

Source: Original
Abba Hikima ya bayyana cewa tambayoyin sun zama masu muhimmanci musamman ganin yadda rundunar ta amince a bainar jama’a cewa taron ya halatta kuma ba ya buƙatar izinin ’yan sanda.
APC ta gargadi Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da barin burin siyasa ya rinjayi dattijantakarsa bayan ya kira Shugaba Bola Tinubu da “Bola”.
Mai magana da yawun kwamitin, kuma Ministan Ma’adanai na Ƙasa, Dele Alake, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Alake ya ce Atiku, wanda ke neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, bai nuna ladabi da girmamawar da ake tsammani daga tsohon mataimakin shugaban ƙasa ba.
Asali: Legit.ng


