Kasurgumin Dan Bindiga Ya Tsalle Tarkon Sojoji, Ya Ci Gaba da Matsawa Mutane a Zamfara

Kasurgumin Dan Bindiga Ya Tsalle Tarkon Sojoji, Ya Ci Gaba da Matsawa Mutane a Zamfara

  • Mazauna garin Wuya da ke Karamar Hukumar Anka a Jihar Zamfara na cikin fargaba bayan wa’adin biyan harajin N40m ga yan bindiga ya ƙare
  • Mazauna sun ce sun biya N30m, amma har yanzu jagoran dabad ’yan bindiga Kachalla Nasanda na bukatar su cika N10m
  • Sun yi zargin cewa Nasanda da mutanensa sun hana zirga-zirga a wasu hanyoyi tare da lalata gadoji kafin su nemi a biya kuɗin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Fargaba ta ƙaru a garin Wuya da ke Karamar Hukumar Anka a Jihar Zamfara, bayan mazauna yankin sun gaza biyan ragowar Naira miliyan 10 na harajin da yan bindiga suka kakaba masu.

Ana zargin cewa jagoran dabar ’yan bindiga, Kachalla Nasanda, ne ya kakaba musu harajin Naira miliyan 40, amma sun biya Naira miliyan 30 daga ciki.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda Nasanda ya takurawa jama'a

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Leadership cewa sun yi nasarar tara N30m daga cikin kuɗin da aka nema, amma wa’adin biyan ragowar N10m ya riga ya ƙare. Hakan ya sa suka shiga fargabar abin da ka iya biyo baya.

Sun bayyana cewa suna jin kamar an barsu su kaɗai, ba tare da wani taimako ba, a lokacin da suke fuskantar wannan matsala.

A cewarsu, Nasanda da mutanensa ne suka kakaba musu harajin bayan zargin kama wasu daga cikin ’yan ƙungiyarsu.

Mazauna sun ce sun tara kuɗin ne ta hanyar sayar da amfanin gonakinsu da kuma neman taimakon kuɗi daga ’ya’yansu da ke aiki a birane.

Sun ƙara da cewa yanzu sun sayar da dukkan hatsi da kayayyakin amfanin gona da suka ajiye, amma har yanzu dan bindigar na jiran ragowar N10m

Shugaban Anka bai san da batun ba

Da aka tuntuɓi shugaban Karamar Hukumar Anka, Bashar Musa Anka, ya ce babu wanda ya kai masa rahoton lamarin, ko a hukumance ko a wajen aiki.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yan bindiga sun rutsa sarki da wasu bayin Allah suna cikin Sallah

Ya ce: “Babu wanda ya kawo mini rahoton wannan batu, kuma ban san da shi ba. Babu wanda ya sanar da ni, ko ta hanyar hukuma ko ba ta hanyar hukuma ba.”

Da aka tambaye shi game da yanayin tsaro a garin Wuya, Bashar ya ce yana yawan tattaunawa da hukumomin tsaro.

Ya bayyana cewa yana tuntuɓar kwamandan bataliyar sojoji da ke yankin maimakon tattaunawa kai tsaye da mazauna garin.

Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa an gayyaci mazauna Wuya zuwa wani shiri a garin Anka, amma har zuwa lokacin da yake magana ba su isa wurin ba.

Nasanda na ci gaba da ayyukansa

Wannan batu ya sake jawo hankali kan ayyukan Nasanda, duk da cewa sojoji sun sanar a watannin baya cewa sun kashe wasu fitattun shugabannin ’yan bindiga da ake kira da Kachalla.

Mazauna yankin sun ce Nasanda na ci gaba da gudanar da ayyukansa a Anka, inda yake kakaba haraji tare da hana mutane shiga wasu yankuna.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Sun yi zargin cewa ƙungiyarsa ta toshe manyan hanyoyin shiga yankin tare da lalata wasu gadoji kafin ta nemi a biya N40m.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ana ci gaba da ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga rundunar sojoji da rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara kan zargin da mazauna yankin suka yi.

Yan sa-kai sun yi artabu da yan bindiga

Kun ji cewa sama da mutane 50 sun mutu yayin wata rangama mai zafi.tsakanin ’yan bindiga da ’yan sa-kai a jihar Zamfara.

Majiyoyi sun ce ’yan sa-kai daga kauyen Zoma da ke karamar hukumar Bukkuyum sun yi wa ’yan bindigar kwanton-bauna, suna kashe da dama daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262