APC Ta Yi Matsaya kan Girmama Atiku da ke Kiran Tinubu da 'Bola'

APC Ta Yi Matsaya kan Girmama Atiku da ke Kiran Tinubu da 'Bola'

  • Jam’iyyar APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da barin burin siyasa ya rinjayi yadda yake mu’amala da Shugaba Bola Tinubu
  • Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben APC, Dele Alake, ya ce kiran shugaban kasar da “Bola” maimakon amfani da mukaminsa bai dace ba
  • APC ta ce za ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ’yan Najeriya, nasarorin gwamnatin Tinubu da shirye-shiryen jam’iyyar yayin neman wa’adin mulki na biyu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC ta soki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan yadda yake kiran Shugaba Bola Tinubu da, “Bola”, maimakon amfani da mukaminsa na shugaban kasa.

Kwamitin yakin neman zaben APC ya zargi Atiku, wanda yake neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC, da barin burin siyasa ya rinjayi mutuncin da ya kamata ya nuna a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa Ministan Ma’adanai, Dele Alake, wanda shi ne mai magana da yawun kwamitin, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

APC ta soki Atiku

Alake ya ce ana sa ran tsohon mataimakin shugaban kasa da kuma wanda ke neman shugabancin kasa zai nuna ladabi da girmama hukumomin da kundin tsarin mulki ya ba iko.

Ya ce kwamitin ya damu da yadda Atiku ke kiran Tinubu da “Bola”, yana mai cewa hakan bai dace da matsayin shugaban kasar ba.

Atiku ya sha kiran shugaban kasar da sunansa na farko, tare da bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin gwamnati mai salon “Yahoo Yahoo”, da kuma zarginta da yin karya.

Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban kasar ya taba yin maganganun da ke nuna shakku kan ko Tinubu ya yi karatu a makaranta.

Alake ya ce tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaben shugaban kasa na baya, ya bari gaba da siyasa da tsananin burin mulki su shafi yadda yake magana da yadda yake gudanar da harkokinsa a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Cakwakiyar da ke zaben gwamnan Adamawa duk da tasirin Fintiri, Atiku da Ribadu

Atiku Abubakar a gidan shi
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa ya kuma zargi Atiku da nuna halin da bai kamata matasan ’yan siyasa su yi koyi da shi ba.

APC ta bukaci a girmama Atiku

Duk da sukar da ta yi wa Atiku, kwamitin yakin neman zaben APC ya bukaci shugabanninta, masu magana da yawunta, mambobinta da kungiyoyin magoya bayanta su ci gaba da nuna masa girmamawar da ta dace da shi.

Alake ya ce APC jam’iyya ce da ke da akidar ci gaba da kuma mutunta al’adun Afirka, don haka ba za ta bi hanyar da ta zargi Atiku da bi ba.

Ya bayyana cewa yakin neman zaben jam’iyyar zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya, manufofin APC, nasarorin gwamnatin Tinubu da sauransu.

APC ta ce Tinubu zai yi nasara

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa kuri’un jin ra’ayin jama’a da jam’iyyar ta gudanar sun nuna cewa Tinubu na kan gaba wajen samun nasara.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya zafafa da ya kwatanta Tinubu da dakikin dalibi

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce jam’iyyar ta gudanar da bincike a jihohi daban-daban tare da tattara alkaluman da ke nuna Tinubu ya fi abokan hamayyarsa samun goyon baya.

Da aka tambaye shi ko sakamakon binciken ya nuna cewa Tinubu zai lashe zaben 2027, shugaban APC ya amsa da cewa, “Tabbas!”

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng