Matatar Mai: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Kenya Ya Gargadi Dangote
- Wani dan takarar shugaban ƙasar Kenya, Patrick Osoi, ya gargaɗi attajirin Najeriya, Aliko Dangote, kan shirin gina matatar mai
- Osoi ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekara mai zuwa, zai bai wa ’yan kasuwar Kenya damar gina matatar mai
- Ana shirin gina matatar a Lamu, Kenya, wadda za ta riƙa tace ganga 700,000 na ɗanyen mai kullum, amma rikicin filaye ya kawo cikas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nairobi, Kenya - Ɗan takarar shugaban ƙasar Kenya, Patrick Osoi, ya gargadi hamshaƙin ɗan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote.
Osoi ya yi gargadin ne tare da bukatar Dangote ka da ya yi gaggawar fara aikin gina matatar mai a Kenya.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya fara yaɗuwa ranar Lahadi, lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a wani taron ƙungiyar Lions Movement, cewar Punch.
Dalilin Osoi na gargadin Dangote
Osoi ya bayyana cewa idan aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar Kenya a shekara mai zuwa, zai dogara da ’yan kasuwar cikin gida wajen gudanar da aikin.
Ɗan takarar ya bayyana cewa Kenya tana da ’yan kasuwa masu ƙarfin tattalin arziki da za su iya gina matatar mai ba tare da dogaro da attajirin ɗan Najeriya ba.
Osoi ya ce:
“Ina so in gaya wa Aliko Dangote cewa, don Allah kada ka yi gaggawar fara gina matatar mai, domin idan aka rantsar da ni shugaban ƙasar Kenya a shekara mai zuwa, za ka koma Najeriya.
“Mu ’yan Kenya muna da ’yan kasuwa da za su iya fara gina matatar mai. Muna kuma da ’yan kasuwa a ƙasarmu waɗanda za su iya gudanar da wannan aiki. Wannan shi ne abin da muka tsaya a kai. Wannan ita ce cibiyar dukkan ƙungiyoyi.”

Source: Facebook
Shirin gina matatar Dangote a Kenya
Jawaban Osoi sun zo ne a daidai lokacin da Dangote ke shirin gina matatar mai ta dala biliyan 16 a Lamu, ƙasar Kenya.
Ana sa ran matatar za ta iya tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana, wanda zai taimaka wajen samar da man fetur ga Kenya da sauran ƙasashen Gabashin Afirka.
A ranar 30 ga Satumba, 2026, Dangote da shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, sun gudanar da bikin aza harsashin ginin matatar.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran kammala aikin ginin matatar man cikin kusan watanni 40.
Rikicin filaye ya kawo cikas ga aikin
Duk da haka, shirin ya fuskanci adawa daga wasu mazauna yankin saboda batutuwan mallakar filaye, biyan diyya da kuma damuwar da suka nuna kan illolin muhalli.
Wata kotun Kenya ta kuma bayar da umarnin a ci gaba da barin abubuwa yadda suke a halin yanzu yayin da ake ci gaba da shari'ar rikicin mallakar filayen da aikin ya shafa.
Zuba jarin da Dangote ke shirin yi na daga cikin manyan ayyukan masana'antu da ake sa ran za su ƙara ƙarfin tace mai a Afirka, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu
Ana kuma sa ran aikin zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron makamashi a yankin da rage dogaro da man fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.
Dangote: Yan sanda za su zuba jari
Mun ba ku labarin cewa Asusun fanshon ’yan sandan Najeriya na nazarin yiwuwar saka jari a matatar Dangote domin faɗaɗa hanyoyin samun riba da kare kuɗaɗen fansho.
Ta ce za ta haɗa hannayen jari, kamfanonin zuba jari, ababen more rayuwa da makamashi, saboda raguwar ribar asusun bankuna.
Hukumar ta ce ta samu matsakaicin ribar kashi 23 zuwa 24 cikin 100 duk shekara cikin shekaru biyar.
Asali: Legit.ng

