An Nadi Wayoyin Su El Rufai, An Zarge Shi da Ware Naira miliyan 800 Zai Ba Jami’an EFCC
- Da alamun jami’an tsaro sun nadi wayoyin mutanen Nasir El-Rufai wanda yanzu ake shari’a da shi
- Wani ma’aikaci da DSS ta kira ya bada shaida ya ce an ware $600, 000 da aka shirya ba jami’an EFCC
- Lauyan El-Rufai ya kalubalanci shaidar da Segun Kayode ya bada, amma bai iya yin nasara a kotu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Wani jami’in tsaro da ke binciken bayanan na’urorin zamani a Hukumar DSS, Segun Kayode ya bada shaida a gaban kotu.
Da ya bada shaida a kotu, Segun Kayode ya zargi Nasir El-Rufai, da wasu mutanensa da ware $60,000 domin biyan jami’an EFCC.

Source: Facebook
An bada shaida a kan Nasir El-Rufai
Punch ta ce a ranar Talatar nan da aka koma kotu, jami’in ya fada wa alkali an tanadi miliyoyin domin biyan jami’an Hukumar EFCC.
DSS ta kira shi ya gabatar da shaida a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Kawo, karkashin jagorancin Mai Shari’a Darius Khobo.
Ya ce an ware $500,000 domin biyan jami’an hukumar, yayin da aka tanadi $100,000 domin a sallami wani saboda a hana bincike.
Ta ina aka samu bayanai a kan El-Rufai?
An gano wadannan bayanai ne a wasu hirarrakin waya da aka nada kuma aka bincika ta hanyar fasahar tantance bayanan na’urorin zamani.
Mai binciken ya shaida wa kotun cewa hirar sun kunshi tattaunawa kan zargin kokarin hana EFCC binciken wani kamfani mai suna Singularity.
Ya ambaci lauyan nan AU Mustapha da Mista Jimi Lawal da Bashir El-Rufai a matsayin mutanen da aka ambata a cikin hirarrakin da aka ji.
A cewarsa, an umurci Mustapha da Lawal su gana da wani Ahmadu Sule domin cire kudin da yake Singularity yadda aka yi wa kamfanin Olam.
Mai bada shaidan ya kara da cewa an tattauna yiwuwar rufe kamfanin a Najeriya da Mauritius, inda ake zargin Hukumar NFIU tana bincikensa.

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
Kayode ya kuma yi zargin cewa hirarrakin sun kunshi tattaunawa kan yadda za a hana jami'an EFCC binciken wani kamfani mai suna HIS.
Idan da gaske ne, an sa hannun jarinsa a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York.
Lauyan Malam El-Rufai ya kalubalanci shaidar DSS
Rahoton PM News ya ce lauyan El-Rufai, Paul Erokoro (SAN), ya yi korafi kan shaidar Kayode.
Ya ce ba a saka sunan mai binciken da takaitaccen bayanin shaidarsa cikin takardun shaidun da masu gabatar da kara suka mika ba.
Erokoro (SAN) ya ce ya kamata a sanar da bangaren kariya shaidun da za a gabatar a kansa idan ana so a yi gaskiya ne a shari’ar.
Kotu ta yarda shaidan DSS ya yi bayani
Sai dai babban lauyan Hukumar ICPC, Ayodeji Adedipe (SAN), ya ce kotun ce ta aika wa Kayode sammacin zuwa bayar da shaida.
Saboda haka ya ce rashin saka sunansa a takardun ba yana nufin ba zai iya bayar da shaida ba.
Bayan sauraron bangarorin biyu, alkali ya amince Kayode ya ci gaba da bayar da shaidarsa, muddin za a iya jefa masa tambayoyi.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: Jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi ɓarin wuta a jihar Kaduna
Daga baya, kotun ta dage shari’ar zuwa ranakun 30 ga Nuwamba da 1 ga Disamba, 2026, bayan an yi awanni kusan takwas ana zama.

Source: Facebook
Lauyoyi 68 sun zama SAN a 2026
Kamar yadda labari ya zo, lauyoyi 67 da suka gawurta wajen aikin shari’a suka samu karin matsayi zuwa SAN a shekarar bana.
Farfesa Nnamdi Onyeka Obiaraeri wanda malamin lauyoyi ne a jami’a shi ma ya samu matsayin duk da kasancewarsa malamin lauyoyi.
Sagir Gezawa Suleiman Esq. daga jihar Kano yana cikin sababbin SAN da Alkalin alkalai, Kudirat Kekere-Ekun ta rantsar a Kotun koli.
Asali: Legit.ng
