Jerin Sababbin Manyan Lauyoyin Najeriya 68 da Suka Samu Matsayin SAN a 2026
- Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Kudirat Kekere-Ekun, ta rantsar da sababin manyan lauyoyi 68 a kasar nan
- A Kotun koli aka tabbatar da su a matsayin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN) a Birnin tarayya na Abuja
- Kudirat Kekere-Ekun ta gargadi sababbin SAN din da aka rantsar din da su guji bata sunan lauyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCT, Abuja - Shugabar alkalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun ta rantsar da sababbin manyan lauyoyi da suka zama SAN.
An samu sababbin SAN wanda yake nuna lauya ya kai matakin koli a harkar shari’a wajen aiki ko a bangaren karantarwa.

Source: Twitter
Gidan talabijin Channels a ranar Litinin ya rahoto cewa an samu sababbin manyan lauyoyi har 68 a shekarar 2026/2027.
Kekere-Ekun ta rantsar da wadannan gogaggun lauyoyi ne a bikin da aka yi domin yin maraba da sabuwar shekarar shari’a.

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
Kwamitin shari’a na LPPC ya amince a kara wa wadannan lauyoyi matsayi a wani zama da aka yi a Abuja a Yulin 2026.
SAN: Alkalin alkalai ta gargadi lauyoyin
An rantsar da su ne a Kotun koli da hudubar su guji bata kima da martabar aikinsu da yin ba daidai ba.
Mai shari’a Kekere-Ekun ta ce ana ba da wannan matsayi ne ga fitattun lauyoyi da suka nuna kwarewa ko fitattun malamai.
Alkalin alkalan ta bukaci wadanda suka zama SAN su dage wajen aiki, tana cewa matsayin karin nauyi ne ya rataya a kansu.
Punch ta ce jerin yana kunshe da lauyoyi 67 da kuma wani malami a jami’a kuma farfesa, Nnamdi Onyeka Obiaraeri.
An ji Shugabar alkalan kasar tana kira ga lauyoyin da su zama abokin koyi ga masu tasowa.
Sababbin lauyoyin da suka zama SAN
Lauyoyin da suka zama SAN su ne:
- Ibrahim Gamdeh Adamu
- Jude Chukwuemeka Okafor
- Godwill Achibong Umoh
- Sunday Samuel Obende
- Adebayo Olugbenga Adaralegbe
- Jimson Ejovi Okodaso
- Olalekan Lawrence Bade-John
- Olaotan Thomas Olusegun
- Philemeon Audu Daffi
- Adenrele David Adegborioye
- James Eromosele Agbonhese
- Alexander Nduka Muoka
- Onome Okodiya
- Emmanuel Akunke Akomaye
- Ikhide Ehighelua
- Mas’ud Mobolaji Alabelewe
- Ogunmuyiwa Olayinka Balogun
- Anthony Auditz Iroagalachi
- Mohammed Tajudeen Mohammed
- Odion Peter Odia
- Gbemiga Adaramola
- Moses Okoh Onyilokwu
- Charles Azubuike Obodozie
- Hakeem Obafemi Agaba
- Bimbo Felix Atilola
- Okechukwu Steve Emelieze
- Joshua Demilade Olaniyan
- Igonikon Abiola Adekunle
- Christian Nnadozie Nwokorie
- Sadiku Momoh Ilegieuno
- Sarafa Kolawole Idowu
- Olujoke Enitan Aliu
- Oliver Onyenucheya Amuzie
- Adebisi Emmanuel Adeniyi
- Faruk Abdullah
- Sagir Gezawa Suleiman
- Ifeanyi Godwin Ezeuko
- Adebayo Folorunsho Ologe
- Sabiu Gumba Adamu
- Eric Keme-Egolukumor Omare
- Soibi Ideriah Ovia
- Somina Peter Johnbull
- Chinedum Ikenna Umeche
- Emmanuel Eghiegba Ekhasemomhe
- Mohammed El-Hassan Sheriff
- Junaidu Bello Marshall
- Olawale Sunday Fapohunda
- Adebiyi Alaba Adetoboye
- Senior Sulyman Ibrahim
- Agba Eimunjeze
- Ayobamidele Oyekunle Akande
- Adetunji Taiwo Adedoyin Adeniyi
- Olamide Moigbotoluwa Adekunle
- Umaru Yunusa
- Akorede Habeeb Lawal
- Darlington Nnabuike Ozurumba
- Nnaemeka Francis Patrick Egonu
- Kayode Orire Omosehin
- Mitchel Akinrinsola Aribisala
- Bolu Agbaje Akadri
- Oluwaseun Asimiyu Alao
- Olugbenga Olusanya Ajala
- Mustapha Olayinka Ajenifuja
- Afees Hassan Adebayo
- Mohammed Abiodun Adelodun
- Jonathan Akintola Makinde
- Olajide Salami
Na karshe a jerin shi ne Nnamdi Onyeka Obiaraeri wanda shi ba lauya ba ne da yake shiga kotu, malamin shari’a ne a jami’a.
68. Nnamdi Onyeka Obiaraeri
Asali: Legit.ng
