Matsalar Tsaro: Jirgin Yakin Sojojin Saman Najeriya Ya Yi Ɓarin Wuta a Jihar Kaduna
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai hari kan wuraren da ake zargin ’yan ta’adda ne a Tudun Rijana da ke Jihar Kaduna
- An gudanar da aikin ne a ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, bayan samun bayanan sirri kan taron wasu ’yan bindiga a yankin
- Rundunar ba ta bayyana adadin waɗanda aka kashe ko suka jikkata a harin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Rundunar Sojin Sama ta Operation FANSAN YAMMA, ta kai hari kan wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a Tudun Rijana, Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Jirgin yakin rundunar sojin Najeriya ya yi ɓarin wuta a wurin ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa wasu ’yan bindiga sun taru a yankin.

Source: Twitter
Masani kuma mi sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a wani rahoto da y wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
An gudanar da aikin ne a ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, ta amfani da jirgin yaƙi samfurin A-29 Super Tucano, bayan kwamandan rundunar sojin saman ya bayar da umarnin mayar da martani cikin gaggawa.
Yadda jirgin ya fito fakiyar hafsoshi
A cewar bayanan aikin, jirgin ya fara rakiyar wani ayarin motocin da ke ɗauke da Babban Kwamandan Runduna ta 1 da kuma Kwamandan Rundunar Sojin Sama, daga Kaduna zuwa Maraban Rido, tare da sa ido daga sama.
A yayin rakiyar, ma’aikatan jirgin sun ci gaba da sa ido kan ayarin motocin ta hanyar gani da kuma sadarwa ta rediyo, yayin da suke bincika wuraren da ke kewaye domin gano duk wata barazana.
Daga bisani, an sauya aikin jirgin zuwa Tudun Rijana bayan bayanan sirri sun nuna cewa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne, waɗanda ba a san adadinsu ba, sun taru a yankin.
Jirgin sojoji ya yi luguden wuta
Rahotanni sun ce ma’aikatan jirgin sun hango waɗanda ake zargin, waɗanda suka yi ƙoƙarin tserewa tare da neman mafaka bayan sun lura da jirgin.
Jirgin ya yi amfani da makaman da ke ɗauke da shi wajen kai hari kan wuraren da aka gano waɗanda ake zargin suna ciki, sannan ya sake zagaya yankin daga sama domin duba halin da ake ciki.

Source: Original
Aikin ya nuna yadda Rundunar Sojin Sama za ta iya haɗa ayyukan kare ayarin motocin jami’an tsaro, sa ido daga sama da kuma mayar da martani cikin gaggawa ga sabbin barazanar tsaro a cikin tafiyar jirgi guda.
Sai dai bayanan aikin ba su bayyana adadin waɗanda ake zargin ’yan ta’adda ne da aka kashe ko suka jikkata a harin ba.
Najeriya ta sayo sababbin jiragen yaki
Kun ji cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sanya hannu kan wani muhimmin yarjejeniya da Bell Textron na Amurka domin ci gaba da shirin sayen jiragen yaƙi 12 na AH-1Z Viper.
Babban hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce jiragen za su ƙara ƙwarewar aiki da ƙarfin rundunar wajen tunkarar barazanar tsaro.
Asali: Legit.ng
