Yadda Kotu Ta Sake Hana Nasir El Rufai Beli da Aka Gano Karya a Takardun Asibiti
Nasir El-Rufai ya sake neman Babban kotun jiha da ke Kaduna ta ba shi beli domin ya bar hannun hukumar ICPC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Lauyoyin tsohon gwamnan sun fake da cewa yana fama da cutar daji don haka dole sai an yi masa aiki a kasar waje
Da aka je kotu, hukumar babban asibitin kasa na Abuja ta nuna ba ta san da zaman El-Rufai ko ciwon da yake yi ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Babban kotun jihar Kaduna da ke sauraron shari’ar Nasir El-Rufai da ICPC ta yi zama game da neman beli da ake ta yi.
A wannan karo ma dai, alkali ya ki bada belin tsohon gwamnan na Kaduna kamar yadda lauyan da yake kare shi ya shigar da bukata wajen sa.

Source: Getty Images
ICPC ta koma kotu da Nasir El-Rufai
The Cable ta kawo rahoto a ranar Alhamis cewa Malam Nasir El-Rufai ya roki alkalin babban kotun ya ba shi beli da sunan bai da lafiya.
Bukatar belin wanda shi ne na uku da tsohon gwamnan ya gabatar bai samu shiga ba kamar yadda jawabin da ICPC ta fitar ya yi nuni.
Alkali Darius Khobo ya yi fatali da bukatar ne tun a farkon makon nan duk da cewa El-Rufai ya fake da cewa yana bukatar zuwa asibiti.
Lauyoyin tsohon gwamna sun kai takardar asibiti
ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta ce an gabatar da wata takarda da babban asibitin kasa na Abuja ya bada a matsayin hujjar rashin lafiya.
Hukumar ta shaida cewa ‘dan siyasar ya yi ikirarin an same shi da cutar daji na ‘Prostate’ wanda ya rika, saboda haka wajibi ne a yi masa aiki.
Lauyoyin El-Rufai sun gabatar da takardar asibiti, suna cewa la’akari da wannan cuta da ta ke damun shi, dole ya ziyarci asibitocin ketare.
A cewar lauyoyin da ake kara, babu wurin da za a iya yin wannan magani duk Najeriya don haka ake neman belin da zai bada damar barin kasa.

Source: Getty Images
Hukumomin asibitin Abuja sun kunyata El-Rufai
Da aka zauna a kotun, lauyoyin masu kara sun gabatar da hujja daga Muhammad Raji Mahmud wanda shi ne shugaban babban asibitin na Abuja.
Bayanan da aka samu daga Muhammad Raji Mahmud sun nuna cewa babu takardar Malam Nasir El-Rufai a asibitin da yake cewa an duba shi.
Likitan yake cewa wanda ake kara bai da wani kati, bai da lamba, kuma ba a taba duba shi a can ba.
Alkali ya hana beli amma ya sassauta wa El-Rufai
Ganin haka ne alkali ya yi fatali da takardar rashin lafiyar da aka kawo, ya yi hukunci cewa an fitar da shi ne ba tare da sanin hukumar asibitin ba.
Idan har asibitin ba su san da takadar ba, Mai shari’a Khobo ya ce ba za a kafa hujja da shi ba.
Sai dai rahoton Sahara Reporters ya ce alkali ya umarci ICPC ta ba El-Rufai damar ganin likitocinsa a koyaushe, kuma a raka shi ya je asibiti.
Daga yanzu tsohon ministan na Abuja yana da hurumin ziyartar duk asibitin da yake so a Najeriya amma bai samu beli ko damar barin kasa ba.
Shari'ar tsohon gwamnan Kaduna da ICPC
Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu mutane da kamfanoni shida kamar yadda aka ji labari.
Ana tuhumar su ne da laifuffuka 11 da suka shafi badakalar kwangila, cin hanci, da wanke kudaden haram lokacin da ya yi gwamna a Kaduna.
Zargin da ake yi ya shafi ba da kwangilar girkawa da samar da na'urorin CCTV a birnin Kaduna. Kudin kwangilar ya kai Naira biliyan 8.68.
Asali: Legit.ng


