Zaben 2027: Fitattun 'Yan Siyasa 6 da Suka Tsallake Rijiya da Baya a Jerin 'Yan Takarar INEC
- Wasu ’yan siyasa da suka sauya sheƙa bayan rasa tikitin takara sun bayyana a jerin sunayen INEC na zaɓen 2027
- Hukuncin Kotun Ƙoli kan rajistar mambobin jam’iyya ya janyo shakku kan cancantar wasu ’yan takara a Najeriya
- Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai Mohammed Adamu, Ovie Omo-Agege, Shehu Buba da Saliu Mustapha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Wasu fitattun ’yan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyun siyasa bayan rasa tikitin takara ko samun saɓani kan zaɓen fidda gwani sun bayyana a cikin jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa ko da yake sanya sunayen ’yan siyasar a jerin ya rage wasu daga cikin shakku kan takararsu, hakan bai tabbatar da cewa sun cika dukkan ƙa’idojin doka ba.
Lamarin ya shafi tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu; ɗan takarar gwamnan Rivers, Kingsley Chinda; tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege; Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba; Sanata Saliu Mustapha; da tsohon shugaban Majalisar Dokokin Delta, Victor Ochei.

Kara karanta wannan
Zaben Gwamna 2027: INEC ta fitar da sunayen ’yan takara 16 a Gombe, babu Pantami a ciki

Source: UGC
1. Hukuncin Kotun Ƙoli ya janyo shakku
A ranar 24 ga Satumba, 2026, Kotun Ƙoli ta dawo da wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 da suka wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu ga INEC aƙalla kwanaki 21 kafin zaɓen fidda gwani.
Dokar ta kuma tanadi cewa mambobin da aka yi wa rajista ne kaɗai za su iya kaɗa ƙuri’a ko tsayawa takara a zaɓen fidda gwani.
Hukuncin ya soke wani hukunci da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a watan Yuli a shari’ar da jam’iyyar Zenith Labour Party ta shigar.
Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya ce hukumar na nazarin cikakken kwafin hukuncin. Kwamishinan hukumar, Mohammed Haruna, ya kuma nuna cewa jam’iyyun da suka tsayar da mutanen da ba mambobinsu ba a lokacin neman tikiti na iya fuskantar matsala.
2. Adamu, Chinda da Omo-Agege sun sauya sheƙa
Mohammed Adamu ya fice daga APC kafin zaɓen fidda gwani, sannan ya koma SDP, inda ya samu tikitin takarar gwamnan Nasarawa bayan Musa Angbazo ya janye. Ko da yake jerin sunayen INEC na farko ya amince da Angbazo, magoya bayan Adamu sun ce maye gurbinsa ya gudana bisa ƙa’ida.
A Rivers, Kingsley Chinda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC a ranar 21 ga Mayu. Rahotanni sun ce ya yi rajistar zama mamba a APC a ranar 27 ga Afrilu, amma sanar da ficewarsa daga PDP ya zo ne a ranar 2 ga Yuni, bayan zaɓen fidda gwani. Wannan ya dasa ayar tambaya kan ko yana cikin rajistar mambobin da aka miƙa wa INEC.
Shi kuwa Ovie Omo-Agege ya rasa tikitin takarar Sanatan Delta ta Tsakiya a hannun Ede Dafinone, ya fice daga APC a ranar 22 ga Mayu, sannan ya koma NDC. Jam’iyyar ta ba shi rangwamen zama mamba, kuma ya samu tikiti ta hanyar amincewar juna.
Victor Ochei ma ya koma NDC, wadda ta ba shi rangwame domin ya fafata a zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Delta ta Arewa.
3. Buba da Mustapha sun samu tikitin wasu jam’iyyu
Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba, ya bar takararsa ta gwamna a APC, sannan aka tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar PRP a ranar 25 ga Mayu. INEC ta jera shi tare da Aliyu Tijjani Mohammed a matsayin mataimakinsa.
Saliu Mustapha kuma ya fice daga APC a watan Agusta bayan ya rasa tikitin takarar gwamnan Kwara da na sanata. Daga baya ya koma PDP, inda ya samu tikitin takarar Sanatan Kwara ta Tsakiya ta hanyar maye gurbin ɗan takara.

Kara karanta wannan
Shehu Sani ya bayar da shawara ga Pantami da sauran 'yan takarar da INEC ta cire sunayensu
Daily Trust ta jaddada cewa bayyana sunan ɗan takara a jerin INEC ba hukuncin kotu ba ne kan halaccin yadda ya samu tikitinsa. Saboda haka, har yanzu ana iya kalubalantar wasu daga cikin takardun takarar a kotu.
Yadda aka cire Pantami a jerin 'yan takarar gwama a Gombe
A wani labarin, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da cikakken jerin sunayen ’yan takarar da ta amince da su domin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027.
Jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takara 16 daga jam’iyyun siyasa daban-daban, tare da mataimakansu, shekarunsu, jinsinsu da takardun karatunsu.
Sakatariyar hukumar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ce ta sanya hannu kan jerin sunayen, inda shekarun ’yan takarar suka kama daga 35 zuwa 72.
Asali: Legit.ng
