Sabon Salo: Jam’iyyar Adawa Ta Yi Maraba da Aka Saka Gwamnanta a Kamfen Tinubu

Sabon Salo: Jam’iyyar Adawa Ta Yi Maraba da Aka Saka Gwamnanta a Kamfen Tinubu

  • Jam’iyyar APGA ta taya Gwamna Chukwuma Soludo murnar naɗa shi a kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu
  • APGA ta ce naɗin Soludo ya nuna kyakkyawar alaƙarta da gwamnatin tarayya, tare da bayyana cewa za ta goyi bayan Tinubu
  • Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta goyi bayan Tinubu shugaban ƙasa, yayin da take son ‘yan takararta su lashe kujerun majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta yi magana da aka sabunta kwamitin kamfen Bola Tinubu.

Jam'iyyar ta taya Gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, murnar shigar k cikin jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Bola Tinubu na 2027.

An saka sunan gwamnan adawa cikin kamfen Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Charles Soludo. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

APGA ta taya Soludo murna

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APGA, Ejimofor Opara, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce shigar da Soludo cikin kwamitin ya tabbatar da kyakkyawan shugabancinsa.

Kara karanta wannan

APC ta yi matsaya kan girmama Atiku da ke kiran Tinubu da 'Bola'

Sanarwar ta ce hakan ya nuna jajircewarsa ga manufofin ci gaba da kuma ƙoƙarinsa na samar da haɗin gwiwa tsakanin APGA da gwamnatin tarayya domin amfanin al’ummar Anambra da ’yan Kudu maso Gabas baki ɗaya.

Ejimofor ya ce taken Soludo na kungiyar “Progressives are Working Together” (Masu ra’ayin ci gaba suna aiki tare) ba taken siyasa kawai ba ne, illa gaskiyar tarihi.

Ya ƙara da cewa APGA, a matsayinta na jam’iyya ta farko mai cikakken ra’ayin ci gaba a Najeriya, tana da akida iri ɗaya da ƙungiyar masu ra’ayin ci gaba da ke jagorantar gwamnatin tarayya.

An sake sunayen wadanda za su tallata Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

APGA ta yaba wa ayyukan Bola Tinubu

Ejimofor ya ce wannan haɗin gwiwa ya riga ya samar da alfanun da ake iya gani a Anambra, ciki har da haɗin kai da gwamnatin tarayya wajen ayyukan more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.

Ya bayyana cewa duk da cewa jam'iyyar APGA ce ke riƙe da ikon mulkin Anambra, matsayinta bai canza ba: Tinubu za ta goyi baya a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da take son APGA ta lashe kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

Shettima ya magantu a kan tsoron da 'yan Arewa ke ji a tazarcen Tinubu

Sanarwar ta ce:

“Kwamitin Aiki na Ƙasa na All Progressives Grand Alliance yana taya jagoran jam’iyyarmu kuma Gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, murnar naɗin da ya samu na zama mai kula da yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027 a Anambra.

An saka sanatan PDP a kamfen Tinubu

A wani labarin, an ji cewa APC ta fitar da sabon jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda aka haɗa Nyesom Wike, da gwamnonin adawa.

Bola Tinubu zai jagoranci kwamitin, yayin da Kashim Shettima da Nentawe Yilwatda za su kasance mataimakan shugabanni, tare da Godswill Akpabio.

APC ta naɗa Abdulaziz Yari darakta janar, yayin da Hope Uzodimma zai zama sakatare, domin tsara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.