Atiku Ya Yi Maganar Magudi da aka Ba Yarabawa Manyan Mukamai a INEC

Atiku Ya Yi Maganar Magudi da aka Ba Yarabawa Manyan Mukamai a INEC

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan naɗa mutane biyu Yarabawa don jagorantar muhimman wurare a hukumar INEC
  • Atiku ta bakin kakakin sa, Phrank Shaibu, ya buƙaci bayanin naɗin Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi da Dr. Lawrence Bayode a ma'aikatar ayyukan zaɓe da sashen ICT
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gargaɗi Shugaba Bola Tinubu da ya janye hannunsa daga hukumar zaɓe, yana mai cewa 'yan Najeriya ba za su amince da maguɗi a zaɓen 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna fargaba kan naɗin jami'ai 'yan ƙabilar Yarbawa biyu wajen jagorantar muhimman sassa biyu a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, jigon APC ta aika wasika ga shugaban Amurka kan zaben 2027

Atiku ya buƙaci INEC ta fito fili ta yi bayani kan ka'idojin da aka bi wajen naɗa Mrs. Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi don maye gurbin Magaji Gum a sashen gudanar da zaɓe, gami da Dr. Lawrence Bayode da ke shugabantar sashen ICT.

Atiku Abubakar da Joash Amupitan
Atiku Abubakar a hagu da Joash Amupitan a dama. Hoto: INEC Nigeria|Atiku Abubakar
Source: Twitter

Gargadin Atiku Abubakar kan magudin zabe

Punch ta wallafa cewa Atiku ya jaddada cewa dole Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nisanta kansa daga gudanarwar hukumar INEC domin tabbatar da an gudanar da zaɓe na gaskiya da amintacce ranar 16 ga Janairu, 2027.

Atiku ya ce:

"Waɗannan ma'aikatun su ne ƙashin bayan gudanar da zaɓe. Dole INEC ta yi bayanin waɗannan shawarwari, ta wallafa ƙa'idojin da aka yi amfani da su tare da nuna cewa dukkan naɗi da sauye-sauyen sun bi tsari da cancanta ba tare da kutsen siyasa ba. '
"Yan Najeriya ba za su amince da alƙawura na fatan baki ba kan abubuwa masu muhimmanci kamar waɗannan."
Shugaban INEC a Najeriya
Farfesa Joash Amupitan a ofishin INEC. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Korafi kan samar da kayan zabe

Kazalika, Atiku ya buƙaci hukumar INEC ta bayyana sunayen kamfanonin da aka ba kwangilar buga kayan zaɓe da jihohin da aka ɗauki nauyinsu, tare da nuna matakan tsaro da aka ɗauka don adanawa da raba kayan gabanin zaɓen na 2027.

Kara karanta wannan

2027: INEC ta kawo mafita ga 'yan takarar da aka cire sunayensu

Daily Post ta rahoto cewa Atiku ya gargaɗi hukumar da cewa al'umar Najeriya za su tsaya tsayin daka ta hanyar amfani da hanyoyin demokaraɗiyya don kare ƙuri'unsu daga duk wani yunkuri na tafka maguɗi a zaɓen.

An zargi Obi da alaka da Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya zargi ɗan takarar jam'iyyar NDC, Peter Obi, da sa ran tallafa wa takarar Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC.

Sowore ya yi ikirarin cewa Obi yana jagorantar magoya bayansa a ɓoye zuwa tsarin Atiku saboda dukkansu suna adawa da manufofinsa na gudanar da sauye-sauye.

Ɗan fafutukar ya ƙara zargin cewa Obi yana ƙoƙarin shimfiɗa hanyar zama Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) idan har Atiku ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng