INEC Ta Cire Sunan Sheikh Pantami daga Jerin Sunayen Yan Takarar Gwamna a Gombe
- Sunan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, bai bayyana a jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamnan Gombe ba
- Hukumar INEC ta amince da ’yan takara 16 domin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 6 ga Fabrairu, 2027
- Kotun Ƙoli ta dawo da wasu sassan Dokar Zaɓe ta 2026 da suka hana jam’iyyu tsayar da ’yan takarar da sunayensu ba sa cikin rajistar mambobin da aka miƙa wa INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen yan takarar gwamnan jihar Gombe na karshe gabanin babban zaben 2027.
Hukumar INEC ta cire sunan dan takarar PDP, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami a jerin sunayen yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan jihar Gombe.

Source: Facebook
Legit Hausa ta fahimci babu sunan Pantami a sunayen yan takarar gwamnan Gombe da INEC ta wallafa a shafinta na yanar gizo yau Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2026.
Sunan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, bai bayyana a jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamnan Jihar Gombe ba.
INEC ta fitar da jerin sunayen ne bisa alƙawarin da shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya yi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a farkon makon nan.
A jerin sunayen, an amince da ’yan takara 16 domin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Jerin sunayen ya ƙunshi Bala Bello Tinka na jam’iyyar ADC, Jamilu Isyaku Gwamna na jam’iyyar APC da Babayo Ardo Kumo na jam’iyyar NDC.
Sauran ’yan takarar da ke cikin jerin sun haɗa da Zubairu Mu’azu Halilu na LP, Lamela L. Silas na APM, Ibrahim Jalo Abubakar na PRP da Adamu Mohammed Ma’aji na SDP, da sauransu.

Kara karanta wannan
Kotu ta ruguza lissafin APC da ADC, ta soke zaben fitar da gwani a jihohin Arewa 2
Sai dai sunan Pantami, wanda ya kasance cikin jerin sunayen wucin gadi da aka wallafa a ranar 29 ga Agusta, bai bayyana a sabon jerin ba.
A baya, Pantami ya zama ɗan takarar jam’iyyar PDP bayan ya fice daga APC a ranar 19 ga Mayu. Sai dai Ahmed Mailantarki Mailantarki, ɗaya daga cikin masu neman tikitin takarar PDP, ya ƙalubalanci nasarar Pantami a kotu.
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fitar da ɗan takarar tare da bayar da umarnin gudanar da sabon zaɓe, wanda Pantami ya sake cin nasara.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
