2027: INEC Ta Kawo Mafita ga 'Yan Takarar da aka Cire Sunayensu
- Jam'iyyun siyasa na NDC da SDP sun ɗauki hanyoyi mabanbanta wajen fuskantar matsalar cire sunayen 'yan takarar gwamnoninsu daga jerin ƙarshe da hukumar INEC
- Jam'iyyar NDC ta zaɓi tsarin tattaunawa da amfani da wa'adin kwana 14 da dokar zaɓe ta 2026 ta bayar, yayin da SDP ta riga ta shigar da takardun shari'a a kotu.
- Hukumar INEC ta bayyana cewa ba za ta maida martani kan rahotannin kafafen yada labarai ba har sai an mika mata korafi a hukumance ta hanyar da doka ta tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buƙaci jam'iyyun siyasar da sunayen 'yan takararsu suka ɓace daga jerin ƙarshe na zaɓen 2027 da su gabatar da ƙorafe-ƙorafensu a hukumance.
Rahotanni sun nuna cewa INEC ta bukaci a mika mata korafi maimakon dogaro da rahotannin kafafen yaɗa labarai.

Source: Twitter
Vanguard ta rahoto cewa jam'iyyun NDC da SDP sun ɗauki matsaya mabanbanta kan wannan matsala da ta shafi zaɓen gwamnoni da ke tafe na shekarar 2027.
Matsayar NDC da SDP
Kakakin jam'iyyar NDC, Araba Director, ya bayyana cewa jam'iyyarsu ba ta tafi kotu ba tukunna, inda suke ci gaba da tattaunawa da INEC domin amfani da wa'adin kwana 14 na dokar zaɓe ta 2026 wajen gyara kuskuren da aka samu.
A gefe guda kuma, kakakin SDP na ƙasa, Araba Rufus Abiyegba, ya tabbatar da cewa su riga da sun ɗauki matakin shari'a inda suka shirya rantsuwar kotu don neman Haƙƙinsu ta hanyar shari'a.
Bayan NDC da SDP, sauran jam'iyyu irin su PDP da ADC su ma sun nuna rashin jin daɗinsu. Sunayen 'yan takarar gwamnan PDP a jihohin Oyo da Gombe, na ADC a Cross River, da na SDP a Benue duk ba su fito a jerin da INEC ta fitar ba.
Matsalar 'yan takara a jihohi
A jihar Kano, ɗan takarar gwamna na NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo, da abokin takararsa, Mustapha Rabiu Kwankwaso, sun rasa sunayensu a jerin.

Source: Facebook
Ɗan majalisar wakilai na NDC, Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya bayyana cewa kuskuren fasaha ne na shigar da bayanai kuma jam'iyyar ta sami tabbacin INEC kan warware matsalar.
Haka zalika, ɗan takarar gwamnan NDC a jihar Cross River, John Upan Odey Jr, ya bayyana cewa cire sunansa kuskure ne na ma'aikata wanda ya shafi jihohi da dama.
Pantami ya mika wa INEC korafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa lauyoyin ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ta ƙalubalanci cire sunansa daga jerin ƙarshe da INEC ta fitar.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 12 ga Oktoba da aka aike wa Shugaban INEC, Joash Amupitan, lauyoyin sun ba hukumar wa'adi zuwa ranar Laraba domin sake buga sunan Pantami a matsayin halattaccen ɗan takara.
Lauyoyin sun jaddada cewa cire sunan ɗan takarar da aka riga aka zaɓa ikon kotu ne kawai ba na hukumar zaɓe ba, domin aikin INEC shi ne lura da gudanar da zaɓe kawai.
Asali: Legit.ng

