Sarkin Musulmi Ya Ce za Su Matsawa Gwamnati Lamba kan Tsadar Rayuwa
- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce shugabannin Musulmi za su ja hankalin masu mulki kan wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta
- Ya bukaci shugabannin siyasa da su dauki matakan inganta rayuwar talakawa, yayin da tsadar abinci, sufuri da man fetur ke kara nauyi ga jama’a
- Sultan ya kuma gargadi matasa kan bari a yi amfani da su wajen ta’addanci, fashi da makami ko rikicin siyasa domin biyan bukatun wasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce shugabannin Musulmi za su ci gaba da jawo hankalin shugabannin siyasa kan matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta tare da matsa musu su dauki matakan inganta rayuwar al’umma.
Sultan ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekaru 100 da kafuwar makarantar Az-Zumratul Adabiyyatul Kamaliyyah da ke Ilorin, wadda marigayi Sheikh Muhammad Kamaldeen Al-Adabiyy, muftin farko na Ilorin, ya kafa.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce shugabannin addini suna sane da korafe-korafen jama’a kan halin da ake ciki, kuma za su yi kokarin isar da sakon ga masu rike da madafun iko.
Maganar Sultan kan tsadar rayuwa
Sarkin Musulmin ya ce shugabannin Musulmi za su yi iya kokarinsu wajen sanar da masu mulki matakan da ya kamata su dauka domin saukaka rayuwar talakawa.
Ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyakin abinci, kudin sufuri da man fetur na ci gaba da jefa iyalai cikin matsin tattalin arziki.
Wannan kira na Sultan ya zo ne kwanaki kadan bayan Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), wadda yake jagoranta, ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakan gaggawa domin rage farashin abinci da sufuri.
A cikin sanarwar da majalisar ta fitar bayan babban taronta a Abuja ranar 8 ga Oktoba, ta bukaci gwamnati ta gaggauta aiwatar da matakan rage wa talakawa nauyin tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
Sultan ya bukaci a rika addu’a
Sultan ya bayyana kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta shawo kan matsalolin da take fuskanta, yana mai cewa babu wata matsala da Allah bai sanya mata mafita ba.
Ya bukaci ’yan Najeriya su yawaita addu’a domin Allah Ya kawo sauki, tare da yi wa Shugaban Kasa Bola Tinubu, gwamnonin jihohi, shugabannin kananan hukumomi da sauran masu mulki addu’ar samun ikon yin daidai..
Ya kuma bukaci Musulmi su kasance masu kyawawan halaye da zaman lafiya da makwabtansu, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.

Source: Facebook
Sultan ya ce mutum ba zai kasance Musulmi nagari ba idan ba ya kaunar makwabcinsa, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da kyautata mu’amala tsakanin al’umma.
Gargadi ga matasa kan siyasa
Sarkin Musulmin ya gargadi matasa kan bari wasu mutane su yi amfani da su wajen tayar da rikicin siyasa, fashi da makami ko ta’addanci domin biyan bukatunsu na siyasa ko kudi.
Ya ce ya kamata matasa su guji shiga ayyukan da za su cutar da su da sauran al’umma, su kuma mayar da hankali kan abubuwan da za su taimaka wajen ci gaban kasa.
A cewarsa, bikin cika shekaru 100 da kafuwar makarantar wata dama ce ta duba nasarorin da ta samu da kuma hanyoyin inganta gudummawarta wajen koyar da ilimi da tarbiyya.
Ya yaba wa shugabannin makarantar tare da bayyana cewa zai duba hanyoyin tallafa wa ci gabanta ta hanyar tattaunawa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Kiran Shettima ga 'yan Arewa
A wani labarin, kun ji cewa Kashim Shettima, ya yi kira ga ’yan Arewa da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin zarcewa a 2027.
Shettima ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa Arewa ta ji tsoron tazarcen Tinubu, yana mai cewa yankin ya amfana sosai da mulkinsa na farko.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi wata tawaga daga kungiyar Arewa for Tinubu (A4A), wadda ta kai masa ziyarar ban girma.
Asali: Legit.ng

