Shettima Ya Magantu a kan Tsoron da 'Yan Arewa ke Ji kan Tazarcen Tinubu
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Arewa su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin samun nasarar zaɓen 2027
- Shettima ya ce Arewa ta amfana da nade-naden mukamai da manyan ayyukan raya ƙasa na gwamnatin Tinubu, kuma za ta ƙara amfana idan ya samu wa’adi na biyu
- Tawagar ƙungiyar Arewa for Asiwaju, karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, ta kai ziyara fadar shugaban ƙasa a ranar Lahadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bukaci al’ummar Arewa su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa yankin ba shi da abin tsoro idan Tinubu ya zarce.
Shettima ya yi wannan kira ne ranar Litinin lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wata ƙungiya da ke fafutukar ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Source: Facebook
Stanley Nkwocha ya wallafa a Facebook cewa Shettima ya bukaci shugabannin Arewa su haɗa kai domin samar da ci gaba da inganta rayuwar al’ummar yankin, yana mai cewa waɗannan na daga cikin muhimman manufofin gwamnatin Tinubu.
Aikin da Tinubu ya yi a Arewa
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Arewa ta amfana sosai da gwamnatin Tinubu ta fuskar naɗa mutane a mukamai da kuma ayyukan raya ƙasa.
Ya ce:
“Mu haɗa kai a matsayin al’umma, mu yi aiki domin ci gaban yankinmu da inganta rayuwar jama’armu ta hanyar sake zaɓen wannan gwamnati. Muna amfana, kuma akwai sauran alherin da za mu samu daga wannan gwamnati ta hanyoyi da dama.
“Bankin Noma ya raba Naira biliyan 450 ga ƙananan manoma 700,000 a Najeriya, kuma kusan kashi 70 cikin 100 na waɗanda suka amfana daga shirin ’yan Arewa ne.
“Gwamnatin yanzu tana ƙoƙarin kammala manyan ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na ƙasar. Ina tabbatar muku cewa shugaban ƙasa yana son Arewa, kuma zai yi aiki domin ci gaban yankin.”

Kara karanta wannan
Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu
Maganar Badaru a taron
Tsohon gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, wanda shi ne darakta-janar na ƙungiyar Arewa for Asiwaju, ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun tabbatar da cewa Arewa ta taka rawar gani wajen sake zaɓen Tinubu.
Badaru ya bayyana cewa ƙungiyar na shirin ganawa da malaman addinin Musulunci da Kiristanci, da sauran manyan ’yan Najeriya domin bayyana musu dalilan da suka sa suke ganin ya kamata a mara wa tikitin Tinubu da Shettima baya a 2027.
Shekarau ya bayyana shirin ƙungiyar
Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ƙungiyar da ta taimaka wajen zaɓen Tinubu a 2023 za ta sake yin irin wannan ƙoƙari a 2027.
Shekarau ya bayyana cewa sun sha ganawa da gwamnonin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da za su taimaka wajen sake zaɓen shugaban ƙasa.
Shekarau ya kuma gayyaci Shettima domin ƙaddamar da ginin ofishin ƙungiyar a hukumance ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2027.

Source: Facebook
Manyan da suka halarci taron
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsoffin gwamnonin Plateau, Joshua Dariye da Sanata Simon Lalong; tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame.
Punch ta wallafa cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello; tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema; da tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda ma sun hallara.
Sauran sun haɗa da Hajiya Hadiza Bala Usman, da shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, da wasu jami’an gwamnati da mambobin ƙungiyar.
Adelabu na PC har yanzu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya musanta rahoton da ke cewa ya yi kira ga ’yan Najeriya su ƙi jam’iyyar APC.
Adelabu ya bayyana rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya da yaudara. Ya ce an ɗauko wani ɓangare ne na bidiyon hirar da ya yi a 2022.
Wannan martani ya zo ne kwana guda bayan wani bidiyon tsohuwar hirar tasa ya sake bayyana a ranar Asabar, inda ya yi magana kan jam’iyyun siyasa.
Asali: Legit.ng

