Zaben 2027: Sarkin Musulmi Ya Aika da Muhimmin Sako ga Matasan Najeriya

Zaben 2027: Sarkin Musulmi Ya Aika da Muhimmin Sako ga Matasan Najeriya

  • Sarkin Musulmi ya gargaɗi matasan Najeriya da su guji bari a yi amfani da su wajen tayar da fitina saboda siyasa ko neman kuɗi
  • Ya buƙaci ’yan Najeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu’a, ciki har da Shugaban Ƙasa da gwamnoni, domin samun mafita ga ƙalubalen ƙasar
  • Sarkin ya yi kira ga Musulmi su kyautata wa maƙwabtansu ba tare da la’akari da bambancin addini ba, yayin da ya yaba da gudummawar makarantar Az-Zumratul Adabiyyatul

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Ilorin, jihar Kwara - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya aika da sakon gargaɗi matasan Najeriya.

Sarkin Musulmin ya gargadi matasan Najeriya da kada su bari a yi amfani da su wajen aikata ayyukan ’yan daba saboda neman ribar siyasa ko ta kuɗi.

Sarkin Musulmi ya ba matasa shawara
Mai alfarma Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Sarkin Musulmin ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoban 2026 a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

"Ba cin mutuncin kowa," Gwamna ya ce auna da abiin da za su tallata APC wurin yan Najeriya a 2027

Mai alfarma Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi jawabin ne yayin bikin rufe bukukuwan cika shekaru 100 da kafuwar makarantar Az-Zumratul Adabiyyatul ta Larabci da Ilimin Addinin Musulunci.

Marigayi Sheikh Muhammad Kamalud-deen Al-Adabiy, wanda ya kafa ƙungiyar Ansarul Islam Society of Nigeria, ne ya kafa makarantar.

Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin Musulmin ya ce:

“Ina ƙalubalantar matasanmu da kada su bari a yi amfani da su a matsayin ’yan daba ta kowace hanya, ko don samun ribar siyasa ko ta kudi.”

Sarkin Musulmi ya buƙaci addu'a ga shugabanni

Sarkin Musulmi ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu’a, ciki har da Shugaban Ƙasa da gwamnoni, yana mai cewa Allah ne ke da mafita ga ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya jaddada muhimmancin kyawawan ɗabi’u ga Musulmi, tare da kira gare su da su ƙaunaci maƙwabtansu kamar yadda suke ƙaunar kansu, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa kan duban jinjirin watan Musulunci a Najeriya

"Ya kamata dukkanmu mu zama Musulmi nagari ta hanyar kyautata wa maƙwabtammu, ko da kuwa ba sa bin addininmu. Haka kuma, ya kamata mu riƙa yi wa shugabanninmu addu’a domin su yi abubuwan alheri ga dukkanmu.” In ji shi.

Sarkin ya ƙara da cewa Musulmi suna ƙaunar kowa, kuma bai kamata su ɗauki kansu a matsayin waɗanda suka fi sauran mutane ba.

"Mu Musulmi ne, kuma muna ƙaunar kowa. Ba mu zo nan domin mu ce mun fi kowa ba. Ya kamata shugabanninmu su ƙara ƙoƙari."
“Mun san matsalolinmu, amma Allah ne yake da mafita gare su. Allah ne yake ba mutum ko ƙasa wadata, kuma shi ne yake ƙaddara akasin hakan.”

Sarkin ya yaba da gudummawar makarantar

Sarkin Musulmi ya yaba wa marigayi Sheikh Muhammad Kamalud-deen Al-Adabiy saboda hangen nesa da gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimin addinin Musulunci.

Ya kuma nuna godiya ga ci gaban da makarantar ta samu tun bayan kafuwarta, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da taimaka mata.

“Muna godiya ga Allah da ya ba wannan makaranta damar ci gaba. Za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya domin taimaka wa wannan makaranta.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi da 'yan bindiga suka hallaka jami'in tsaro a Plateau

Sarkin Musulmi ya bayar da shawara ga matasa
Sarkin Musulmi a wajen taro Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Getty Images

Sarkin Musulmi ya yi kira ga Hausawa, Fulani

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga Hausawa da Fulani da su kawo ƙarshen rashin yarda da ke tsakaninsu.

Sarkin Musulmin ya ce ya kamata al’ummomin biyu su ƙara kusantar juna, su kuma ƙarfafa fahimtar juna domin samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng