Sarkin Musulmi Ya Juyo kan Siyasa, Ya Yi Masu Gargadi Mai Zafi
- Sarkin Musulmi ya ce bai dace a yi amfani da kudaden da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa wajen daukar mutane aikin Hajji ko ziyartar Kudus ba
- Ya bukaci shugabannin addinai su hada kai da hukumomin yaki da cin hanci domin dakile rashawa da kuma tabbatar da bin doka ba tare da nuna bambancin siyasa ko addini ba
- Ya kuma gargadi malaman addini da su kula da kalamansu a lokacin zabe, su rika yi wa shugabanni addu’a maimakon tada fitina ko rarrabuwar kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati.
Sarkin Musulmin ya gargade su da su guji daukar nauyin aikin Hajji ko ziyartar wurare masu tsarki a Makka da Kudus da kudaden da aka samu ta hanyar sata ko cin hanci.

Source: Twitter
Sarkin Musulmin ya yi wannan gargadin ne ranar Laraba, 23 ga watan Satumban 2026 a Abuja, yayin bude taron masu ruwa da tsaki da Majalisar Kasa ta Huldar Addinai (NIREC) ta shirya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
‘Allah ba Ya son cin hanci’
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Sarkin Musulmi ya jaddada cewa ya kamata shugabannin addinai su hada kai da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa domin dakile matsalar da ke addabar kasa.
Ya ce shugabannin addinai na da rawar da za su taka wajen yaki da rashawa saboda Allah ba Ya son cin hanci da rashawa.
“Mu a matsayinmu na shugabannin addinai, dole mu yaki cin hanci da rashawa saboda Allah Madaukakin Sarki ba Ya son cin hanci."
“Ba za ka iya satar kudi ka tura mutane Kudus ko Makka da kudaden rashawa ba, sannan ka yi tunanin Allah zai karbi ayyukanka. Allah ba Mai rashawa ba ne, saboda haka ba za ka yi amfani da kudin rashawa wajen Hajji ko wani abu daban ba,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Ya bukaci EFCC ta hukunta masu laifi
Sarkin Musulmi ya bukaci Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta dauki kwakkwaran mataki kan duk wanda aka samu da hannu wajen cin hanci da rashawa, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ko addininsa ba.
“Duk wanda ke da hannu, ko ’yan’uwanmu ne, ’yan’uwanmu mata ne, iyayenmu ne ko abokanmu, ya kamata ya fuskanci doka."
“Idan mutum yana fuskantar doka, kada ku zo ku ce min shi Fasto ne na wata coci ko babban limami ne na wata masallaci. Ba ma son jin haka,” in ji Sarkin Musulmi.
Ya kuma bukaci EFCC ta gudanar da ayyukanta ba tare da tsoma bakin siyasa ba.
Ya bukaci fahimtar juna tsakanin addinai
Sarkin Musulmi ya yabawa NIREC, yana mai cewa majalisar wata muhimmiyar kafa ce wajen karfafa tattaunawa da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Ya ce irin wadannan taruka na yau da kullum suna da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasa.
Gargadi ga malaman addini a lokacin zabe
Sarkin Musulmi ya kuma gargadi malaman addini da su kula da kalaman da suke yi a kan mimbari, musamman a lokacin gudanar da zabubbuka.
Ya bukaci malaman su rika yi wa shugabanni a kasa addu’a, maimakon amfani da wuraren ibada wajen tunzura jama’a, yada rarrabuwar kai ko kai hare-haren kalamai kan masu rike da mukaman gwamnati.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi ya bayar da shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shawarci ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan wajen tantance alkawuran ’yan siyasa.
Ya kuma gargadi ’yan siyasa da kada su mayar da matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta wani makami na siyasa yayin yakin neman zaɓe.
Asali: Legit.ng

