Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Duban Jinjirin Watan Musulunci a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Duban Jinjirin Watan Musulunci a Najeriya

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Musulmi su fara shirin duban jinjirin watan Jumada Ula na shekarar 1448
  • Sultan ya buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan ya sanar da dagacin garinsu ko na ƙauye mafi kusa domin isar da sakon
  • Sakamakon aikin duban watan zai tabbatar da ranar fara watan Jumadal Ula, yayin da watan Ramadan je kara gabatowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Ƙungiyar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya nemi a far duban jinjirjn watan Jumada Ula.

Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai a faɗin ƙasar nan da su fara shirin duban jinjirin watan Jumadal Ula na shekarar 1448 bayan hijira a ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ware gwamna 1 a Arewa, ta yaba masa kan ayyukan alheri

Sarkin Musulmi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III a fadarsa da ke Sakkwato Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Shafin Daular Usmaniyya na Facebook ya wallafa sanarwa da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wanda shi ne shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, ya sanya wa hannu.

Sultan ya umarci fara duban wata

Sanarwar ta bayyana cewa ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, ta yi daidai da ranar 29 ga watan Rabi’us Thani na shekarar 1448 bayan hijira.

An ware ranar domin gudanar da aikin duban wata a faɗin Najeriya, don tabbatar da lokacin shigar watan Jumada Ula.

Sarkin Musulmi ya buƙaci Musulmi a dukkan sassan Najeriya da su fita duba da yammaci bayan faɗuwar rana domin ganin ko za a iya hango jinjirin watan.

Yadda za a tura sakon ganin wata

Sanarwar ta kuma umarci duk wanda ya yi nasarar ganin jinjirin watan da ya gaggauta kai rahoto ga dagaci/magajin gari na ƙauye mafi kusa, domin isar da bayanin ga Sarkin Musulmi.

Kara karanta wannan

Musulmi sun yi rashi: Malamin Musulunci ya rasu a Adamawa bayan fama da jinya

Wannan umarni ya yi daidai da tsarin Musulunci na dogaro da ganin sabon jinjirin wata wajen tantance farkon watannin kalandar Musulunci, bisa tabbatarwar hukumomin addini da abin ya shafa.

Ana sa ran Musulman da suka ga jinjirin watan za su bayar da sahihan bayanai ta hanyar ssrakunan gargajiya da na addini da aka amince da su, domin taimakawa wajen tantancewa da sanar da sakamakon a hukumance.

Sarkin Musulmi, a matsayinsa na babban jagoran musulmai a Najeriya kuma Shugaban Ƙoli na NSCIA, yana taka muhimmiyar rawa wajen daidaita sanarwar ganin wata.

Sarkin Musulmi ya nemi hadin kai

Saboda haka, sanarwar ta buƙaci haɗin kai tsakanin malaman addinin Musulunci, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran Musulmi domin tabbatar da sahihanci da tsari wajen isar da rahotannin ganin wata.

Wata.
Yadda ake hango jinjirin wata a sararin samaniya Hoto: Inside The Haramain
Source: Twitter

Majalisar Masarautar Sakkwato ta buƙaci al’ummar Musulmi da su dakonci sanarwa a hukumance bayan kammala aikin duban watan, domin sakamakon ne zai tabbatar da lokacin shigar wa Jumada Ula na shekarar 1448 bayan hijira.

Sultan ya yi nasiha ga musulmi

Kun ji cewa Sarkin Musulmi ya bayyana cewa babu wanda ya kamata a tilasta wa shiga Musulunci, yana mai kira ga Musulmi da su mutunta hakkoki da ’yancin mabiyan sauran addinai.

Muhammad Sa'ad Abubakar ya kuma yi kira ga Kiristoci da Musulmi da su guji zagin juna, yana mai cewa mutunta juna na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262