Hukumar Fanshon Ƴan Sanda Za Ta Zuba Hannun Jari a Matatar Dangote
- Asusun fanshon ’yan sandan Najeriya na nazarin yiwuwar saka jari a matatar Dangote domin faɗaɗa hanyoyin samun riba da kare kuɗaɗen fansho
- Ta ce za ta haɗa hannayen jari, kamfanonin zuba jari, ababen more rayuwa da makamashi, saboda raguwar ribar asusun bankuna.
- Hukumar ta ce ta samu matsakaicin ribar kashi 23 zuwa 24 cikin 100 duk shekara cikin shekaru biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja Hukumar Asusun fanshon ’yan sandan Najeriya na nazarin damar saka hannun jari a matatar Dangote da masana’antun sarrafa man fetur.
Hakan na cikin ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin saka jari da kuma tabbatar da ci gaba da samun riba ga jami’an ’yan sanda da ’yan fansho.

Source: Facebook
Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar, Muhammed Dutse, ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja yayin bikin makon hidimar abokan ciniki na 2026, cewar Punch.
Dalilin shirin zuba jari a matatar Dangote
Dutse ya ce hukumar kula da asusun fanshon na neman wasu hanyoyin saka jari, saboda raguwar kudaden ruwa na iya rage ribar gargajiyar saka jari.
Ya ce:
“Kamar yadda kuke gani a baya-bayan nan, ana yawan magana kan matatar Dangote da masana’antun sarrafa man fetur. Don haka, mu ma muna kallonta.”
Ya bayyana cewa dabarar saka jarin kamfanin za ta haɗa hannayen jari da kamfanonin zuba jari, kuɗaɗen ababen more rayuwa da sauran kadarorin saka jari.
Dutse ya ce akwai kuɗaɗen kamfanonin zuba jari, kuɗaɗen ababen more rayuwa da sauran hanyoyin saka jari da za su iya samar da riba mai kyau.
Ya ƙara da cewa kamfanin na duba damar saka jari a kasuwar hannayen jari, ciki har da hannayen manyan kamfanonin Najeriya.

Source: Twitter
Dutse ya ce hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin kare kuɗaɗen fansho da kuma samar da riba mai gasa ga masu karɓar fanshon.
Dabarar da ke cikin zuba hannun jari
Wannan bayani ya zo ne yayin da sha’awar saka jari a matatar Dangote ke ƙaruwa, musamman bayan matakan faɗaɗa mallakar katafaren kamfanin.
Dutse ya ce dabarar rarraba saka jari ta zama muhimmiyar hanya bayan sauye-sauyen manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya, CBN.
Ya ce sauye-sauyen na iya yin tasiri kan ribar da masu kula da asusun fansho za su samu daga wasu hanyoyin saka jari, cewar Vanguard.
A cewarsa, hukumar za ta ƙara duba damar saka jari a ababen more rayuwa, kamfanonin zuba jari da fannin makamashi domin ƙarfafa matsayinta.
Ya ce:
“Dabararmu ta haɗa dukkan waɗannan hanyoyin saka jari. Ba mu dogara kawai da abin da bankuna ke ba mu ba.”
Dutse ya ce hukumar ta samu matsakaicin ribar shekara-shekara da ya kai kusan kashi 23 zuwa 24 cikin 100 cikin shekaru biyar da suka gabata.
Gwamna zai saya wa malmai hannun jari
An ji cewa Gwamnatin Kwara ta shirya sayen hannun jarin matatar Dangote ga mata malamai, domin karfafa musu guiwa.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce za a bai wa mata malamai hannun jari 10,000, tare da shirin fadada tsarin.
Gwamnatin ta kuma ware N120m ga fitattun malamai, shugabannin makarantu da jami’an ilimi domin yaba kokarinsu.
Asali: Legit.ng

