Bayan Hadarin Ondo, Jirgin Sojin Najeriya Ya Sake Samun Matsala a Sama

Bayan Hadarin Ondo, Jirgin Sojin Najeriya Ya Sake Samun Matsala a Sama

  • Jirgin sama NAF ya sauka a wata gona da ke yankin Utur Tse-Igboji a Makurdi bayan kammala aikin tallafa wa dakarun ƙasa wajen farmakar masu garkuwa da mutane
  • Hedikwatar NAF ta ce matukin jirgin ya yanke shawarar yin saukar kariya ne bisa ƙa’idojin tsaro bayan kammala aikin yaƙi
  • Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan hadarin jirgin NAF 931 a Igbokoda, jihar Ondo, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 25 da ke cikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana cewa ɗaya daga cikin jiragenta masu saukar ungulu ya yi “saukar kariya” a wata gona da ke jihar Benue.

Rundunar ta ce jirgin ya kammala aikin tallafa wa dakarun ƙasa a wani samame da aka kai wa waɗanda ake zargi da yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ogbadigbo.

Kara karanta wannan

Jirgin saman Najeriya ya yi saukar gaggawa a gona bayan hadarin jirgi a Ondo

Jirgin Najeriya a sama
Jirgin Najeriya a sama. Hoto: NAF
Source: Twitter

Jirgin NAF ya sauka a gona

The Cable ta wallafa cewa shaidun gani da ido sun ce jirgin ya sauka a wata gona da ke yankin Utur Tse-Igboji, cikin garin Makurdi.

Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce aikin sojan ya gudana ne kusa da iyakar jihar Enugu da Benue, inda jirgin ya taimaka wajen tarwatsa ayyukan wasu miyagun mutane tare da bai wa dakarun ƙasa damar ci gaba da kutsawa yankin.

NAF ta ce an bi ƙa’idojin tsaro

Ejodame ya ce bayan kammala aikin, matukin jirgin ya yanke shawarar yin saukar kariya yayin da yake kan hanyarsa ta komawa sansanin.

Ya ce jirgin ya sauka ne kimanin mil 10 daga filin jirgin, matakin da aka ɗauka bisa ƙwarewar matukin da kuma ƙa’idojin aiki da tsaro da rundunar ta tanada bayan kammala ayyukan yaƙi.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rasa ransa bayan caka masa wuka a Jigawa kan N500 kacal

Rahoton TVC ya nuna cewa NAF ta ce jirgin ya koma sansanin da ya ke aiki lafiya bayan lamarin.

Lamarin Benue ya faru ne kwanaki biyu bayan wani jirgin NAF mai lamba NAF 931 ya yi hatsari a yankin Igbokoda, ƙaramar hukumar Ilaje ta jihar Ondo.

Jirgin NAF da ya yi hadari
Jirgin sojin Najeriya da ya yi hadari a Ondo. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Jirgin ATR-42 ɗin yana gudanar da wata tafiya ta yau da kullum daga Benin zuwa Legas lokacin da ya faɗa cikin wata fadama kusa da wani sansanin sojojin ruwa a ranar Litinin, 5 ga Oktoba.

NAF ta tabbatar da cewa mutane 25 ne ke cikin jirgin, waɗanda suka ƙunshi ma’aikatan jirgi biyar da fasinjoji 20, kuma babu wanda ya tsira daga hatsarin.

Wadanda suka mutu a Ondo

A wani labarin, kun ji cewa rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta fitar da sunayen ma’aikatan jirgi biyar da fasinjoji 20 da suka rasu a hadarin jirgin NAF 931 da ya faru a Igbokoda, jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan jirgin da suka rasu sun haɗa da MI Aburime, AP Man-Ugwueje, IS Bako, Abubakar A da Uguru HC.

NAF ta ce jirgin yana gudanar da aikin yau da kullum ne daga Benin zuwa Legas lokacin da hatsarin ya faru, kuma ba a samu wani wanda ya tsira ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng