Jirgin Saman Najeriya Ya Yi Saukar Gaggawa a Gona bayan Hadarin Jirgi a Ondo

Jirgin Saman Najeriya Ya Yi Saukar Gaggawa a Gona bayan Hadarin Jirgi a Ondo

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya yi wani irin sauka a wata gona a Benue
  • Rundunar ta ce jirgin ya tallafa wa farmakin da aka kai kan masu garkuwa da mutane a Ogbadigbo, kusa da iyakar Enugu da Benue
  • Lamarin ya faru kwanaki biyu bayan hatsarin jirgin NAF a Ondo, inda mutane 32, ciki har da ma’aikatan jirgin, suka mutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benue - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya yi saukar kariya a Benue bayan kammala aikin tallafa wa dakarun ƙasa.

Shaidun gani da ido sun ce jirgin ya sauka a wata gona da ke al’ummar Utur Tse-Igboji, a ƙaramar hukumar Makurdi.

Jirgin sama ya samu matsala a Benue
Taswirar jihar Benue da jirgin sama ya samu akasi. Hoto: Legit.
Source: Original

Ehimen Ejodame, daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na NAF, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Bayan hadarin Ondo, jirgin sojin Najeriya ya sake samun matsala a sama

Ejodame ya ce aikin sojan ya mayar da hankali kan masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ogbadigbo, kusa da iyakar Enugu da Benue.

Ya ce aikin ya tarwatsa ayyukan miyagun mutanen tare da taimaka wa dakarun ƙasa wajen ci gaba da kutsawa cikin yankin.

Sanarwar ta ce bayan kammala aikin cikin nasara, matukin jirgin ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen yin saukar kariya.

An ce jirgin ya sauka kusan mil 10 na ruwa daga filin jirgin, bisa tanade-tanaden tsaro da ake bi bayan ayyukan yaƙi.

Rundunar ta ce matukin jirgin ya ɗauki matakin ne domin bin ƙa’idojin aiki da tsaro da aka tanada bayan kammala ayyukan yaƙi.

NAF ta kuma tabbatar da cewa jirgin mai saukar ungulun ya koma sansaninsa bayan saukar da ya yi a Benue.

Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan wani jirgin NAF ya yi hatsari a Igbokoda, ƙaramar hukumar Ilaje ta Ondo.

Jirgin ya ɗauki fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai lokacin da ya faɗa cikin wani fadama da ke gaban sansanin sojojin ruwa.

Jirgin, samfurin ATR-42 mai lambar wutsiya NGR 931, ya faɗa cikin fadamar ne da sanyin safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

Hukumar fanshon ƴan sanda za ta zuba hannun jari a matatar Dangote

A ranar Talata, Ejodame ya ce Sunday Aneke, babban hafsan sojin sama, ya bayyana hatsarin a matsayin babban abin takaici ga rundunar da ƙasa.

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a samu wani mutum da ya tsira daga hatsarin jirgin da ya faɗa a Ondo ba.

Bayan wannan mummunan hatsari, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a ƙasa domin tunawa da jami’an sojin sama.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.