Atiku Ya Magantu kan Tsadar Kayan Noma, Ya Fadi Mafita tare da Sukar Tinubu
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza tallafa wa manoma
- Atiku ya ce matsalolin tsaro da tsadar noma da samar da kayayyaki na ƙara jefa manoma da ’yan kasuwa cikin wahala, yayin da ƙasar ke rasa kuɗin shiga daga noma
- Ya yi wannan zargin ne yayin da alkaluman cinikayyar noma suka nuna cewa Najeriya ta samu gibin N56.13bn a farkon 2026, bayan ta samu rarar N740.27bn a 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda yake cewa harkar noma ta koma baya.
Atiku ya ce gwamnatin ta gaza samar da yanayin da zai ba manoma damar noma cikin tsaro, yayin da masana'antun sarrafa amfanin gona ke fuskantar tsadar samar da kayayyaki.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Atiku ya yi magana ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar.
Yadda noma ta ci baya
Atiku ya ce bayanan cinikayyar ƙasar sun nuna cewa Najeriya ta samu rarar N740.27bn daga cinikayyar kayan noma a farkon 2025, amma an samu gibin N56.13bn a farkon 2026.
A cewarsa, hakan ya nuna sauyi na N796.40bn cikin shekara guda, yayin da fitar da kayan noma zuwa ƙasashen waje ya ragu da kashi 33.3 cikin 100.
Atiku ya ce bai kamata a ɗaura alhakin matsalar kan yadda ’yan Najeriya ke shigo da kaya daga ƙasashen waje kawai ba.
Ya ce gwamnati na da alhakin bayyana abin da ta yi domin ƙara yawan kayan da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje, da kuma taimaka wa manoma da masana'antun cikin gida.
Atiku ya kuma ce noma ba za ta bunƙasa ba idan manoma ba su da tsaro, yayin da masana'antun ba za su iya aiki yadda ya kamata ba idan farashin samar da kayayyaki ya yi tsanani.

Kara karanta wannan
"Yan Najeriya ba su cancanci haka ba," Atiku ya sake aika sako mai ɗaga hankali ga Tinubu
Batun fitar da amfanin gona
Atiku ya ce Najeriya na noma amfani, amma wasu ƙasashe ne ke yin ƙarin sarrafa shi tare da samun mafi yawan ribar da aikin ke samarwa.
“Mun noma amfanin gona a nan, amma wani ne ke yin ƙarin sarrafa shi, ya gina kasuwanci a kansa sannan ya samu mafi yawan riba. Daga nan Tinubu ya yi magana kan samar da ayyukan yi, alhali masana'antun Najeriya sun koma baya,”
In ji shi.
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙara tsadar samar da kayayyaki, sannan ta kira wahalhalun da suka biyo baya da sunan gyara.

Source: Getty Images
Maganar Atiku kan tallafi
Atiku ya kuma bayyana shirin da ya ce zai aiwatar wajen tallafin man fetur da aka tace a Najeriya, inda ya ce manufar ita ce sammar da sauki.
Ya ce tallafin zai shafi kayayyakin man fetur da aka tace a matatun man Najeriya, ciki har da ƙananan matatun mai, yayin da man fetur da aka shigo da shi daga waje ba zai amfana da tallafin ba.
Ya ce idan ya samu damar kafa gwamnati, zai dawo da wani tsari na tallafin samar da man fetur a cikin gida daga ranar farko, tare da tallafa wa manoma da masu sarrafa amfanin gona.
“Za mu noma shi a nan. Mu sarrafa shi a nan. Mu tace shi a nan. Mu samar da ayyukan yi a nan. Mu sauƙaƙa rayuwa,”
In ji shi.
Babachir ya caccaki Atiku
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa zai fi son Shugaba Bola Tinubu a kan Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce idan Atiku ya zama shugaban ƙasa, Najeriya na iya shiga wani yanayi na rugujewa cikin rudani.
Babachir da ya bar ADC bayan Atiku ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, ya ce abin da ya fuskanta wajen aiki da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ne ya sauya matsayarsa.
Asali: Legit.ng

