'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Dan Agajin Izala, Bala Lau Ya Yi Magana

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Dan Agajin Izala, Bala Lau Ya Yi Magana

  • Wani mamba na kungiyar JIBWIS, Abubakar Yusuf Sokoto, na cikin jami'an tsaro biyar da suka rasa rayukansu a harin ’yan bindiga a jihar Zamfara
  • Marigayin, wanda ke aiki a matsayin ɗan sanda, ya rasu ne a ranar Lahadi yayin da wasu ’yan bindiga suka yi wa tawagar jami’an tsaro kwanton ɓauna
  • Shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalansa da sauran mambobin kungiyar bisa wannan babban rashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Zamfara – Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta yi alhini kan rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta, Abubakar Yusuf Sokoto, wanda ya rasu a harin ’yan bindiga a jihar Zamfara.

Marigayin, wanda ke aiki a rundunar ’yan sandan Najeriya, ya rasa ransa ne yayin da wasu ’yan bindiga suka kai wa tawagar jami’an tsaro hari a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna bayan yi wa 'yan sanda kwanton bauna a Zamfara

Dan agajin Izala Sheikh Bala Lau
Abubakar Yusuf Sokoto a hagu, Sheikh Bala Lau a dama. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

JIBWIS ta wallafa a shafinta na Facebook cewa maharan sun yi wa jami’an kwanton ɓauna ne a lokacin da suke tafiya a cikin motoci uku.

JIBWIS ta miƙa saƙon ta’aziyya

Shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ne ya miƙa saƙon ta’aziyyar ƙungiyar ga iyalai da ’yan uwan marigayin.

A cikin saƙon ta’aziyyar, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa Abubakar Yusuf Sokoto, wanda ke riƙe da muƙamin leken asiri agajin Izala, ya rasu ne sakamakon harin bindiga da aka kai masa yayin gudanar da aikinsa na rundunar ’yan sandan Najeriya.

Ya ce wannan babban rashi ne ba ga iyalansa da ’yan uwansa kaɗai ba, har ma da ƙungiyar JIBWIS da al'ummar Musulmi baki ɗaya.

Shugaban ya yi addu'ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya jiƙansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya karɓi shahadarsa, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Ya kuma miƙa ta'aziyya ga iyalansa, abokan aikinsa, shugabannin JIBWIS da dukkan mambobin ƙungiyar, tare da addu'ar Allah Ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda na ganin ƙiyayya, an ƙona motoci a tawagar kamfen dinsa

Sheikh Abdullahi Bala Lau
Sheikh Bala Lau a wajen taro a Abuja. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Yadda aka kai harin

Rahoton Punch ya bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Lahadi, lokacin da jami'an tsaron ke tafiya a cikin motoci uku kafin maharan su yi musu kwanton ɓauna.

Wani ɗan sanda da ke cikin tawagar, wanda ya tsira daga harin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun buɗe wuta ba zato ba tsammani kan motar da ke ƙarshen tawagar.

Ciyaman ya rasu a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi, Hon. Mas’ud Aliyu Umar, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a daren Lahadi.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana alhininsa kan rasuwar shugaban karamar hukumar, inda ya bayyana marigayin a matsayin ma'aikacin gwamnati mai kishin al'umma.

An gudanar da sallar jana'izarsa da ƙarfe 2:00 na rana a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026, a fadar Dagacin Mur Mur da ke karamar hukumar Zaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng