Jihohi 31 Sun Kashe Naira Biliyan 45 Wajen Sayen Mai a Wata 6

Jihohi 31 Sun Kashe Naira Biliyan 45 Wajen Sayen Mai a Wata 6

  • Gwamnatocin jihohi 31 a Najeriya sun kashe Naira biliyan 45.04 wajen sayen man fetur na motoci, injinan samar da wutar lantarki da sauransu
  • Kuɗin da aka kashe ya ƙaru da kashi 14.35 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira biliyan 39.38 da jihohin suka kashe a makamancin lokacin shekarar 2025
  • Rahoton ya ce Lagos ce ta fi kashe kuɗi da Naira biliyan 8.93, sai Yobe, Nasarawa, Kano da Ekiti, yayin da Gombe ta kashe Naira miliyan 890.75

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatocin jihohi 31 a Najeriya sun kashe jimillar Naira biliyan 45.04 wajen sayen man fetur na motoci, injinan samar da wutar lantarki da sauran na’urorin aiki tsakanin watan Janairu da Yunin 2026.

Wani bincike da aka gudanar kan rahotannin aiwatar da kasafin kuɗin jihohin na zangon farko da na biyu ya nuna cewa kuɗin ya ƙaru da Naira biliyan 5.65 idan aka kwatanta da Naira biliyan 39.38 da aka kashe a makamancin haka a 2025.

Kara karanta wannan

Yadda Opay, Moniepoint ke tantance lambobi don samun tallafin N50,000

Gwamnonin Najeriya a taro
Gwamnonin Najeriya na taro a Abuja. Hoto: Abdul No Shaking
Source: Facebook

Rahoton Punch ya nuna cewa wannan na nufin jihohin sun kashe kusan Naira biliyan 7.51 a kowane wata, ko kuma Naira miliyan 248.82 a kullum wajen sayen mai.

Mai ya kara tsada sosai

Ƙarin kuɗin da jihohin suka kashe ya zo ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da matsalolin zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.

Rahoton ya nuna cewa farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya tashi daga dala 61 kan kowace ganga a farkon shekarar 2026 zuwa sama da dala 100.

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa farashin man fetur da dizal a Najeriya ya ƙaru da kashi 22.5 da kashi 16 bi da bi a watan Maris, idan aka kwatanta da farashinsu kafin yaƙin.

Binciken ya yi la’akari da kuɗaɗen da aka kashe a zahiri wajen sayen man motocin gwamnati da na injinan samar da wutar lantarki, ba wai kuɗin da aka ware a kasafin kuɗi ba.

Kara karanta wannan

Indonesia: An yi wa shugaban kasa kutse a waya, an saurari maganganun da yake yi

Injina da janareto sun ja kudi sosai

Daga cikin Naira biliyan 45.04 da aka kashe, Naira biliyan 28.52 sun tafi wajen sayen man injinan samar da wutar lantarki da janareto, yayin da Naira biliyan 16.52 suka tafi wajen sayen man motocin gwamnati.

Kuɗin man injina da janareto ya ƙaru da Naira biliyan 3.64, kwatankwacin kashi 14.63, daga Naira biliyan 24.88 da aka kashe a farkon rabin shekarar 2025.

Haka kuma, kuɗin man motocin gwamnati ya ƙaru da Naira biliyan 2.01, kwatankwacin kashi 13.88, daga Naira biliyan 14.50.

Binciken ya nuna cewa injina da janareto sun cinye kashi 63.33 cikin 100 na jimillar kuɗin da aka kashe, tare da kasancewa sanadin kashi 64.38 na ƙarin kuɗin da aka kashe idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Jihohi 24 cikin 31 sun ƙara kuɗin da suke kashewa wajen sayen mai, yayin da jihohi bakwai suka rage kashe kuɗinsu. Jihohi 13 ne suka kashe sama da Naira biliyan ɗaya kowannensu.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Jihohin da suka fi kashe kuɗi

Jihar Lagos ce ta kasance a kan gaba wajen kashe kuɗin sayen mai, inda ta kashe Naira biliyan 8.93, daga Naira biliyan 7.65 da ta kashe a makamancin lokacin shekarar 2025.

Wannan ya nuna ƙarin Naira biliyan 1.28, kwatankwacin kashi 16.79. Jihar ta kashe Naira biliyan 8.26 wajen sayen man injina da janareto, yayin da Naira miliyan 670.20 suka tafi wajen man motoci.

Jihar Yobe ta zo ta biyu da kashe Naira biliyan 3.42, daga Naira biliyan 2.83 a shekarar da ta gabata. Kusan dukkan kuɗin sun tafi ne wajen sayen man injina da janareto, inda aka kashe Naira biliyan 3.39, yayin da motocin gwamnati suka cinye Naira miliyan 35.76.

Nasarawa ta zo ta uku da kashe Naira biliyan 3.29, daga Naira biliyan 2.02 a farkon rabin shekarar 2025. Ƙarin kuɗin ya kai Naira biliyan 1.26, kwatankwacin kashi 62.59.

Jihar ta kashe Naira biliyan 1.77 wajen sayen man injina da janareto, sannan Naira biliyan 1.51 wajen man motocin gwamnati.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Kano da Ekiti sun kashe kudi sosai

Jihar Kano ta kashe Naira biliyan 2.99 wajen sayen mai a farkon rabin shekarar 2026, daga Naira biliyan 2.61 da ta kashe a makamancin lokacin shekarar 2025. Wannan ya nuna ƙarin kashi 14.70.

Daga cikin kuɗin, Naira biliyan 2.62 sun tafi wajen sayen man injina da janareto, yayin da Naira miliyan 368.27 suka tafi wajen man motoci.

Ekiti ta kashe Naira biliyan 2.81, daga Naira biliyan 2.33 a shekarar da ta gabata, wanda ya nuna ƙarin kashi 20.46. Jihar ta kashe Naira biliyan 2.38 wajen sayen man injina da janareto, yayin da motoci suka cinye Naira miliyan 430.95.

Jihar Edo ta kashe Naira biliyan 2.74, inda mafi yawan kuɗin suka tafi wajen sayen man motocin gwamnati, wanda ya kai Naira biliyan 2.36. Wannan shi ne mafi girman kuɗin man motoci da wata jiha ta kashe cikin jihohin da binciken ya ƙunsa.

Jihohin Lagos, Yobe, Nasarawa, Kano, Ekiti da Edo sun kashe kashi 53.69 na jimillar kuɗin da aka kashe a jihohin 31.

Kara karanta wannan

Kamfanin BUA ya tashi da ribar kusan rabin Naira tiriliyan a cikin watanni 9

Ana saka mai a gidan mai
Motoci na shan fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gombe ta kashe Naira miliyan 890.75

Sauran jihohin da suka kashe sama da Naira biliyan ɗaya sun haɗa da Ogun da ta kashe Naira biliyan 2.21, Benue Naira biliyan 1.70, Bauchi Naira biliyan 1.64, Abia Naira biliyan 1.54, Anambra Naira biliyan 1.26, Adamawa Naira biliyan 1.12 da Borno Naira biliyan 1.09.

Gombe ta kashe Naira miliyan 890.75, yayin da Jigawa ta kashe Naira miliyan 997.09, Kwara Naira miliyan 981.75, Bayelsa Naira miliyan 961.68 da Enugu Naira miliyan 914.17.

A gefe guda, Kebbi ce ta fi kowace jiha kashe kuɗi kaɗan, inda ta kashe Naira miliyan 3.06. Oyo ta kashe Naira miliyan 11.54, Kogi Naira miliyan 288.05, Delta Naira miliyan 358.19, yayin da Cross River ta kashe Naira miliyan 371.32.

Cross River ce ta fi samun ƙarin kuɗin kashewa idan aka yi la’akari da kaso, inda kuɗin ya tashi da kashi 353.17 daga Naira miliyan 81.94 zuwa Naira miliyan 371.32.

Kara karanta wannan

Shiri ya yi nisa: An fadi lokacin samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya

An kirkiro rumfunan zabe a jihohi

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi ƙarin bayani kan rahotannin ƙirƙiro sabbin rumfunan zaɓe 453 a faɗin Najeriya.

Hukumar ta ce sauye-sauyen sun biyo bayan hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙiro sababbin mazaɓu a jihohin Kogi, Benue da Delta.

INEC ta ce ba ta gudanar da aikin a ɓoye ba, amma za ta yi cikakken bayani ga masu ruwa da tsaki bayan kammala nazarin dukkan matakan cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng