Bayan Rasa Iko a Majalisar Amurka, Trump Ya Dauko Sabuwar Hanyar Nakasa Iran

Bayan Rasa Iko a Majalisar Amurka, Trump Ya Dauko Sabuwar Hanyar Nakasa Iran

  • Gwamnatin Amurka ta kafa sabuwar rundunar soji mai suna Task Force Iron Gate domin dakile safarar makamai
  • Rundunar za ta mayar da hankali kan hana Iran samun fasahohin da ake amfani da su wajen kera makamai
  • Rahotanni sun nuna cewa Iran ta shigo da makamai, bama-bamai da manyan motoci da darajarsu ta kai dala biliyan biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Gwamnatin Amurka ta sanar da kafa sabuwar rundunar soji domin dakile safarar makamai da wasu kayayyakin da aka kakaba wa kasar Iran takunkumi ta kan iyakokinta da kuma tekun Caspian.

Rundunar mai suna Task Force Iron Gate za ta kasance ne a birnin Tampa da ke jihar Florida, inda za ta hada kai da sauran hukumomin gwamnatin Amurka wajen aiwatar da aikin.

Kara karanta wannan

Amurka ta sa kyautar Naira biliyan 26 tana neman sirrin nukiliyar Iran

Amurka ta sake taso Iran a gaba
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Rahoton Reuters ya bayyana cewa rundunar za ta mayar da hankali kan dakile safarar makamai, fasahohin da ake amfani da su wajen kera makamai da kuma hanyoyin samun kudaden shiga da Washington ke zargin Iran da amfani da su wajen gudanar da ayyukan da ba su halatta ba.

Wannan mataki na zuwa ne bayan Amurka ta shafe watanni tana aiwatar da killace jiragen ruwan Iran, a wani yunkuri na kara matsin lamba kan gwamnatin Tehran.

Iran ta shigo da kayayyakin soji na $2bn

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa Iran ta kafa wata boyayyar hanyar sadarwa ta hukumomin soji domin shigo da kayayyakin yaki da sauran kayan aiki.

Binciken ya nuna cewa kasar ta shigo da makamai, bama-bamai da manyan motocin dakon kaya da darajarsu ta kai akalla dala biliyan biyu tun watan Janairun 2025.

An bayyana cewa kayayyakin sun shiga Iran ta hanyoyi daban-daban, ciki har da jiragen ruwa daga Rasha ta tekun Caspian, manyan motoci daga kasashen Asiya ta Tsakiya da kuma jiragen dakon kaya daga China.

Kara karanta wannan

Matashi ya dauki bindigogi da niyyar kashe Trump a Amurka

Wannan na nuni da yadda Iran ke amfani da wasu hanyoyi wajen kauce wa takunkumin Amurka da kawayenta na Yamma.

Amurka na neman hana Iran safarar makamai
Sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Amurka ta ce ta hana Iran samun $25bn

Kwamandan rundunar sojin Amurka ta CENTCOM, Admiral Brad Cooper, ya ce hada kai da sauran hukumomin gwamnati zai taimaka wajen takaita karfin Iran na samar da kudaden ayyukan ta'addanci da sake gina masana'antun makamai.

A cewar rundunar, killace jiragen ruwan Iran ya hana kasar fitar da danyen mai da darajarsa ta zarce dala biliyan 25, cewar Middle East Online.

Sai dai duk da wadannan matakai, Iran na ci gaba da nuna karfin jure matsin lambar da ake yi mata, yayin da shugabanninta ke kara tsaurara matakan tsaro a cikin kasar.

Shirin Amurka kan kadarorin Iran

An ji cewa kasar Amurka ta fara lissafin asarar da kasashen Larabawa suka yi a yakin da ake yi da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Wata majiya ta bayyana cewa ministan baitul malin Amurka, Scott Bessent, ya umarci a tattara kimar asarar da ƙasashen yankin suka yi.

Rahoton ya ce har yanzu ba a tantance irin kadarorin Iran da za a yi amfani da su ba, yayin da tattaunawar zaman lafiya ke gudana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.