Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Bayani kan Ko Wakili Zai Iya Karba
- Gwamnatin Tarayya ta ce za a biya tallafin Naira 50,000 kai tsaye ga wanda aka yi wa rajista, ta hanyar lambar wayarsa
- Ɗan uwa ko amintaccen mutum zai iya taimaka wa mai cin gajiyar tallafin wajen latsa lambar shiga, amma shi ne zai shigar da PIN ɗinsa
- Gwamnati ta gargaɗi masu cin gajiyar tallafin da kada su bai wa kowa wayoyinsu, PIN ko OTP, ko da kuwa suna amincewa da mutumin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fayyace cewa babu wanda zai iya karɓar tallafin Naira 50,000 na wata-wata a madadin wani mutum, inda ta ce ana tura kuɗin ne ta hanyar lambar wayar wanda aka yi wa rajista.
Wannan bayani na gwamnati ya zo ne domin amsa tambayar da ’yan Najeriya da dama ke yi kan ko ɗan uwa ko wani amintaccen mutum zai iya karɓar kuɗin a madadin wanda aka amince da shi.

Source: Getty Images
Yadda tsarin biyan tallafin yake aiki
A cewar Gwamnatin Tarayya, an tsara tsarin biyan tallafin ne ta yadda wanda aka yi wa rajista shi kaɗai zai iya samun damar karɓar kuɗin.
Tsarin yana da alaƙa kai tsaye da lambar wayar wanda zai amfana da tallafin. Saboda haka, ba za a iya karkatar da kuɗin zuwa wani mutum ko kuma wani ya cire su a madadinsa ba.
Sai dai gwamnati ta amince cewa wani amintaccen ɗan uwa ko mutum na kusa zai iya taimaka wa wanda zai amfana da tallafin wajen latsa lambar da ake amfani da ita domin shiga tsarin.
Wannan taimako ya shafi latsa lambar shiga ne kawai. Gwamnati ta jaddada cewa dole ne wanda aka yi wa rajista da kansa ya shigar da lambar sirrinsa ta musamman, wato Personal Identification Number (PIN).
Abubuwan da bai kamata a yi ba
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi kai tsaye ga duk masu cin gajiyar tallafin da kada su ba wani mutum wayoyinsu ko lambobin sirrinsu.

Kara karanta wannan
Yadda Gwamnatin tarayya take zaɓar waɗanda za su samu tallafin N50,000 a Najeriya
Ta kuma jaddada cewa bai kamata su bayyana wa wani PIN ko lambar tabbatar da shiga sau ɗaya (OTP) ba, ko da kuwa mutumin amintacce ne a gare su.
Gargaɗin ya shafi kowa, har da ’yan uwa na kusa da ke taimaka wa masu cin gajiyar tallafin wajen gudanar da aikin cire kuɗin.
Ana ganin wannan mataki na gwamnati yana da nufin kare masu cin gajiyar tallafin daga masu damfara, domin ba wa wani bayanan shiga asusu na iya ba shi damar kwashe kuɗin ba tare da sanin mai su ba.
Dalilin bayar da tallafin N50,000
Tallafin Naira 50,000 na wata-wata na daga cikin shirye-shiryen tallafin jin ƙai da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar domin taimaka wa ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi.
Gwamnati ta shawarci waɗanda aka amince da su a shirin da su bi ƙa’idojin karɓar kuɗin yadda aka tsara.
Haka kuma, ta bukaci masu fuskantar matsala wajen cire kuɗinsu da neman taimako daga hukumomin gwamnati da aka tabbatar da sahihancinsu, maimakon miƙa bayanan sirrinsu ga wasu mutane.

Source: Twitter
Masu amfana da sauye-sauyen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC Bank Plc da gidauniyar Anap Foundation, Atedo Peterside, ya yi magana kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu.
Atedo Peterside ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu sun fi amfani ga masu hannu da shuni, yayin da suka ƙara tsananta halin rayuwar miliyoyin ’yan Najeriya.
Asali: Legit.ng
