An Kara wa Jami'an INEC Albashi da Alawus yayin da ake Shirin Zaben 2027
- Hukumar INEC ta amince da sabon tsarin albashi da ƙarin alawus ga ma’aikatanta gabanin babban zaɓen shekarar 2027
- Hukumar ta kuma ƙara kuɗin gudanar da ofisoshinta na jihohi da kashi 150 cikin 100, tare da dakatar da hutun shekara ga ma’aikata
- Shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikatan hukumar kan rashin zuwa aiki, nuna son kai ga jam’iyyun siyasa da almundahana da kuɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da sabon tsarin albashi, ƙarin alawus na aiki da kuma ƙara kuɗin gudanar da ofisoshinta na jihohi da kashi 150 cikin 100, a wani mataki na ƙarfafa shirye-shiryen zaɓen 2027.
Hukumar ta kuma umarci ma’aikatanta da su dakatar da zuwa hutun shekara, tare da gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin ladabtarwa kan duk wanda aka samu da sakaci, rashin zuwa aiki, nuna goyon baya ga wata jam’iyya ko almundahana.

Kara karanta wannan
Gaskiya za ta yi halinta: Hukumar DSS ta fara bincike kan zargin da Atiku Abubakar ya yi

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana matakan a ranar Juma’a a Lokoja, yayin wani taron tattaunawa da ma’aikata na shiyyar Arewa ta Tsakiya da tantance shirye-shiryen zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa matakan sun haɗa da inganta jin daɗin ma’aikata, ƙarfafa ayyukan ofisoshin hukumar da kuma samar da kayan aiki domin gudanar da zaɓen da ake sa ran sama da masu rajista miliyan 103 za su shiga.
Hukumar INEC ta yi karin albashi
Amupitan ya bayyana cewa sabon tsarin albashin ma’aikatan INEC mai suna CEMBSS ya fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Ya ce an samar da tsarin ne bayan hukumar ta fice daga tsarin albashin ma’aikatan gwamnati na gama-gari domin samar da tsarin da ya dace da nauyin aikin zaɓe.
Shugaban INEC ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen samar da kuɗin aiwatar da sabon tsarin albashin, yayin da aka amince da ƙarin albashi da alawus.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya
Haka kuma, ya ce daga ranar 1 ga Yuli, 2026, hukumar ta ƙara kuɗin gudanar da ofisoshinta na jihohi da kashi 150 cikin 100 domin sauƙaƙa musu ayyukan yau da kullum.
An samar wa INEC motoci
Dangane da sufuri, Amupitan ya bayyana cewa an raba motocin ɗaukar kaya ga ofisoshin INEC na jihohi da ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.
Punch ta rahoto ya ce hukumar ta kuma sayo motoci kirar SUV guda 20 domin kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs), yayin da sakatarorin gudanarwa za su samu sababbin motoci domin ƙarfafa ayyukansu.

Source: Facebook
Sai dai shugaban INEC ya jaddada cewa inganta jin daɗin ma’aikata da samar musu da kayan aiki dole ne ya kasance tare da ladabi, ƙwarewa da kuma rashin nuna son kai ga jam’iyyun siyasa.
Ya umarci kwamishinonin zaɓe da sakatarorin gudanarwa da su tabbatar da bin diddigin halartar aiki da kuma ɗaukar ma’aikata alhakin ayyukansu.
Maganar takarar Atiku Abubakar a ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta musanta wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta sake amincewa da shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.
Hukumar ta bayyana cewa saƙon bogi ne, tare da yin Allah wadai da amfani da tambarinta da hoton Kwamishinanta na ƙasa, Mohammed Haruna, wajen yaɗa bayanin.
INEC ta buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da saƙon, tare da bin sahihan hanyoyin sadarwarta domin samun ingantattun bayanai kan ayyukanta.
Asali: Legit.ng
