Mummunar Ambaliya Ta Kashe Mutum 633 a Nepal, Ruwa Ya Kwarara China da India

Mummunar Ambaliya Ta Kashe Mutum 633 a Nepal, Ruwa Ya Kwarara China da India

  • Masu aikin ceto a Nepal da China na ci gaba da neman kusan mutane 3,000 da suka ɓace bayan ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu yankunan Himalaya
  • Rahotanni sun ce an gano gawarwaki 633 a kasashen biyu, yayin da ake fargabar wasu daga cikin mutanen da suka mutu za su iya gangarawa zuwa India
  • Hukumomin Nepal sun ce dubban mutane da suka hada da ma’aikatan tashoshin samar da wutar lantarki, masu yawon bude ido na cikin wadanda ba a gani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kathmandu – Masu aikin ceto a Nepal da China na ci gaba da kokarin gano dubban mutanen da suka ɓace kwanaki bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye yankunan Himalaya.

Ambaliyar ruwan ta zo da wani katafaren ganuwar ruwa da laka da tarkace, inda ta shafe kauyuka da dama tare da lalata gidaje da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Kididdigar masana ta nuna fiye da mutum 1,500 ne suka bace a Jihar Yobe

Ambaliyar ruwa a Nepal
Mutane a wajen ambaliyar ruwan Nepal. Hoto: Getty Images
Source: Instagram

Dubban mutane sun bata

CNN ta rahoto cewa sababbin alkaluman da hukumomi a kasashen biyu suka fitar sun nuna cewa adadin mutanen da ba a san inda suke ba ya kusan 3,000, yayin da aka gano gawarwaki 633.

Hukumar kula da bala’o’i ta Nepal ta kara sunayen ma’aikatan tashoshin samar da wutar lantarki 933 cikin jerin mutanen da suka ɓace, baya ga masu yawon bude ido.

Wata kungiyar Red Cross ta ce bala’in ya shafi mutane kusan 93,000, yayin da ake sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu.

Wani wanda ya tsira daga ambaliyar, Buddhi Dangol, ya shaida wa AFP cewa dukkan kauyukan da ke kusa da kogin ruwa ya shafe su.

Daruruwan mutane sun makale

A bangaren Nepal, sojoji sun gano wasu mutane da suka makale a cikin wani rami na aikin samar da wutar lantarki na Trishuli 3A.

Mai magana da yawun rundunar sojin Nepal, Raja Basnet, ya ce an tura jirage masu saukar ungulu guda biyu domin taimaka wa aikin ceto, amma gano bakin ramukan na da matukar wahala.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa fitaccen ɗan kasuwa a masallaci bayan sallar Isha'i

Reuters ta wallafa cewa ya ce an ceto kusan ma’aikata da mazauna yankin 350 daga wurin, amma har yanzu ana kokarin ceto sama da mutum 100 da suka makale.

Hukumomin Nepal sun bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a kasar ya kai 626, yayin da mutane 2,426, ciki har da daruruwan ‘yan kasashen waje, ba a iya samun labarinsu ba.

Hukumomin China sun kuma ce sun kwashe masu yawon bude ido 555 da kuma ‘yan kasar China 499 da suka makale a yankunan da abin ya shafa.

Ambaliyar ruwa Nepal
An ceto wani da ya makale a ambaliyar Nepal. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A India kuwa, hukumomi sun ce an gano gawarwaki bakwai a cikin kogunan da ke kwarara daga Nepal, wadanda ake kyautata zaton mutanen da ambaliyar ta shafa ne.

Sauro ya yi kisa a Jamus

A wani labarin, mun ruwaito cewa ma’aikatan filin jirgin sama biyu a Frankfurt na Jamus sun mutu sakamakon zazzabin cizon sauro, bayan wata barkewar cutar da ta kama ma’aikata shida.

Hukumomin lafiya sun ce ana kyautata zaton sauro mai dauke da cutar ya shigo Jamus ne ta jirgin sama, lamarin da ya haifar da wani yanayi mai matukar wuya.

Hukumomi sun kafa tarkuna a filin jirgin domin kama sauro tare da gudanar da gwaje-gwaje a dakunan bincike domin gano nau’in sauro da kuma asalin inda ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng