A Kula: Bauchi, Jigawa da Wasu Jihohi 26 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

A Kula: Bauchi, Jigawa da Wasu Jihohi 26 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

  • NiMet ta yi sabon gargaɗin yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya daga 11 zuwa 20 ga Yulin 2026
  • Hukumar ta ce ruwan sama da aka samu a farkon watan Yuli ya cika ƙasa da ruwa, lamarin da ke ƙara haɗarin ambaliya
  • An shawarci jama'a da hukumomin agajin gaggawa su ɗauki matakan kariya domin rage asarar rayuka da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da sabon gargaɗi kan yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 26 da babban birnin tarayya Abuja.

NiMet ta bayyana cewa jihohin Bauchi, Jigawa, Taraba, Adamawa, Plateau, Benue, Nasarawa da Kogi na cikin yankunan Arewa da ke fuskantar babban haɗari tsakanin 11 zuwa 20 ga Yulin 2026.

An yi hasashen ambaliyar ruwa
Wasu gidaje da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Najeriya Hoto: Haruna Yahaya
Source: Getty Images

Hukumar NiMet ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

"Ku taimaka": Remi Tinubu ta roki Davido da sauran manyan mawaka a Najeriya

NiMet ta bayyana cewa ci gaba da samun ruwan sama a cikin kwanaki 10 na farkon watan Yuli ya sa ƙasa ta cika da ruwa a sassa da dama na ƙasar, wanda hakan ya rage ƙarfin ƙasar na shanye ƙarin ruwa, tare da ƙara yiwuwar ambaliyar ruwa cikin gaggawa.

Jihohin da ke cikin haɗari

A cikin taswirar hasashen haɗarin ambaliyar ruwa ta kwanaki 10 na biyu na watan Yuli (11–20 ga Yuli, 2026), hukumar ta kuma lissafo jihohin Kwara, Oyo, Ogun, Legas, Osun, Ekiti, Ondo, Delta, Edo, Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Akwa Ibom, Cross River, Rivers da Bayelsa, tare da Abuja, a matsayin wuraren da ke cikin haɗarin ambaliya.

Hukumar ta ce haɗuwar ci gaba da ruwan sama da kuma ƙasa mai cike da ruwa na iya jawo ambaliyar ruwa a wurare masu ƙasa, birane da yankunan da ba su da ingantaccen tsarin magudanar ruwa.

Illolin da ake hasashe

NiMet ta yi gargaɗin cewa ambaliyar na iya kawo cikas ga sufuri ta hanyar mamaye tituna, haddasa cunkoson ababen hawa da kuma hana zirga-zirga a wasu hanyoyi.

Hukumar ta kuma ce ruwan sama mai ƙarfi na iya katse wutar lantarki da hanyoyin sadarwa, yayin da rashin gani sosai lokacin da ake tsananin ruwan sama zai iya jefa masu amfani da hanya cikin haɗari tare da shafar harkokin sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Guguwa mai karfi ta hallaka mutane, ta yi mummunar barna a Yobe

Bugu da ƙari, NiMet ta ce ambaliyar na iya lalata gonaki da amfanin gona a lokacin da noma ke da matuƙar muhimmanci, lamarin da ka iya rage yawan amfanin gona tare da barazana ga wadatar abinci.

Haka kuma, ta yi gargadin cewa muhimman kayayyakin more rayuwa kamar tituna, gadoji da magudanan ruwa na iya samun mummunar lalacewa idan ambaliyar da ake hasashe ta faru.

Wadanne shawarwari NiMet ta bayar?

Hukumar ta bayyana cewa ruwan da ke tsayawa bayan ambaliya na iya ƙara yaɗuwar cututtukan da ruwa ke haddasawa saboda ƙarancin tsafta a yankunan da abin ya shafa.

Domin rage illolin da ka iya faruwa, NiMet ta bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa su rika bibiyar hasashen yanayi da gargaɗin ambaliya tare da ɗaukar matakan kariya kafin a samu ruwan sama mai ƙarfi.

An lissafo jihohin da ake hasashen ambaliyar ruwa
Gidaje cikin ruwa bayan ambaliyar ruwa a Najeriya Hoto: Haruna Yahaya
Source: Getty Images

Hukumar ta kuma yi kira ga hukumomin ba da agajin gaggawa na jihohi (SEMAs) da su ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen tunkarar lamarin tare da haɗin gwiwa da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Hakazalika, ta shawarci al'ummomi su tabbatar da cewa an share magudanan ruwa, bututun kwararar ruwa da hanyoyin ruwa daga shara domin ba wa ruwan sama damar gudana cikin sauƙi tare da rage haɗarin ambaliya a birane.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za a kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

NiMet ta yi hasashen ambaliya

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar NiMet ta yi gargadin cewa jihohi 27 na Najeriya na iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin ranar 1 zuwa 10 ga watan Yulin 2026.

Hukumar ta bayyana cewa ana sa ran mamakon ruwan sama zai ci gaba da sauka a wannan lokaci, yayin da ake kara nutsawa a cikin daminar a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng