Shirin Kifar da Tinubu: Yarjejeniyar da Atiku Ke Shirin Kullawa kan Zaben 2027

Shirin Kifar da Tinubu: Yarjejeniyar da Atiku Ke Shirin Kullawa kan Zaben 2027

  • Wakilan Atiku da Gwamna Seyi Makinde sun gudanar da tarurruka da dama, inda aka samu ci gaba kan yiwuwar haɗin gwiwa a zaɓen 2027
  • Wata majiya a ADC ta Kudu maso Yamma da kuma ɗan takarar APM sun bayyana cewa yarjejeniyar na iya kankama nan ba da jimawa ba
  • Sai dai ba a bayyana sharuɗɗan haɗin gwiwar ko yadda za a warware batun wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wakilan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gudanar da tarurruka da dama.

Wakilan Atiku da Makinde sun gudanar da tarurrukan ne tare da samun matsaya kan yiwuwar haɗa kai domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku na shirin kulla yarjejeniya da Makinde
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Binciken jaridar The Punch ya nuna cewa tattaunawar da ke gudana tsakanin Atiku da Makinde ta bambanta da sauran shawarwarin da shugabannin jam’iyyun adawa ke yi domin fitar da ɗan takara guda da zai fafata da Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fadi halin Peter Obi da ya bambanta shi da saura

Gwamna Makinde, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), ya sha sukar gwamnatin Tinubu, tare da goyon bayan ƙoƙarin shugabannin adawa na kifar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.

Yadda tattaunawar haɗin gwiwar ta fara

A ranar 25 ga Afrilu na wannan shekara, Makinde ya shirya taron shugabannin jam’iyyun adawa a gidan gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan.

A taron ne shugabannin siyasar suka tattauna yiwuwar tsayar da ɗan takara guda domin fafatawa da jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai har yanzu wannan yunƙuri bai haifar da yarjejeniya ba, domin Atiku, Makinde da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, sun ci gaba da riƙe burinsu na neman shugabancin ƙasa.

A ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamban 2026 Makinde ya tabbatar da cewa yana tattaunawa da shugabannin adawa, ciki har da Atiku da Obi.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Arise News, gwamnan ya ce shawarwarin na ci gaba da gudana, kuma sakamakonsu zai iya bayyana ko za su fafata da juna ko kuma su haɗa kai a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Rusa takarar Atiku: Kalubalen da ke gaban ADC kan zaben 2027

“Dangane da abin da za mu gani tsakanin yanzu da lokacin zaɓe, muna iya zama abokan hamayya, ko kuma mu haɗa kai. Ɗaya na iya zama wanda ɗayan ke yi wa aiki.” In ji shi.

Majiyoyi sun ce yarjejeniyar na kankama

Jaridar ta tattaro daga sansanonin Atiku da Makinde cewa akwai yiwuwar manyan ’yan siyasar biyu su haɗa kai.

Wasu manyan ’yan siyasa da ke da masaniya kan tattaunawar sun ce wakilan ɓangarorin biyu sun gudanar da tarurruka da dama, kuma suna samun ci gaba wajen cimma yarjejeniya.

Wani jagoran ADC a Kudu maso Yamma, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya nuna kyakkyawan fata kan nasarar tattaunawar haɗin gwiwar.

Ya bayyana tattaunawar a matsayin sabuwa, mai manufa kuma mai alamar nasara, yana mai cewa nan ba da jimawa ba ’yan siyasar biyu za su bayyana shirinsu a hukumance.

Da aka tambaye shi lokacin da za a sanar da yarjejeniyar, ya yi barkwanci da cewa, “Kafin ranar 16 ga Janairu.”

Haka kuma, wani ɗan takarar APM da ke da masaniya kan tafiyar siyasar Makinde ya shaida wa jaridar cewa gwamnan zai yi aiki tare da Atiku a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Da wace doka alkali ya dogara wurin rushe takarar Atiku da shugabancin ADC

Ya ce alamomi sun nuna cewa haɗin gwiwar na kankama bayan tarurruka da dama da wakilan ɓangarorin biyu suka gudanar, ta intanet da kuma kai tsaye.

A kalamansa:

“Bayanan da muke da su sun nuna cewa haɗin gwiwar Atiku da Makinde abu ne mai yiwuwa, kuma yana kankama. An gudanar da tarurruka da dama cikin makonnin baya-bayan nan, ta intanet da kuma kai tsaye, kuma sun haifar da sakamako mai kyau.
“Abin da ke faruwa ya nuna cewa ɓangarorin biyu sun cimma matsaya kan wasu batutuwa, kuma nan ba da jimawa ba za su bayyana yarjejeniyar.”

Gwamnatin Oyo da ADC sun tabbatar da tattaunawa

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Oyo, Dotun Oyelade, shi ma ya tabbatar da cewa Makinde na tattaunawa da sauran shugabannin adawa.

Sai dai bai tabbatar da cewa gwamnan da Atiku sun cimma wata yarjejeniya ta musamman ba.

Oyelade ya bayyana waɗanda ke cikin shawarwarin a matsayin ƙwararrun ’yan siyasa da suka san yadda siyasar zamani take, musamman dangane da batutuwan da suka shafi gwamnatin Tinubu.

Ya ce Makinde a shirye yake ya haɗa kai da sauran shugabannin adawa idan hakan zai samar da ingantacciyar dama ta magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Akwai kura: An taso Tinubu a gaba kan yunkurin kinkimo bashin N11trn

ADC ma ta tabbatar da cewa jam’iyyun adawa na ci gaba da tattaunawa domin yiwuwar haɗin gwiwa wajen ƙalubalantar APC a 2027.

Atiku da Makinde na tattaunawa
Atiku Abubakar tare da Gwamna Seyi Makinde Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Sakataren Yaɗa Labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa tattaunawar ba ta takaita ga wani ɗan siyasa ko jam’iyya guda ba.

Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labaran Atiku, Phrank Shaibu, shi ma ya tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar na tattaunawa da shugabannin adawa.

Sai dai shi da Bolaji Abdullahi ba su tabbatar da cewa an cimma wata yarjejeniya ta musamman tsakanin sansanonin Atiku da Makinde ba.

Haka kuma, babu wata majiya da ta bayyana takamaiman sharuɗɗan tattaunawar ko tsarin haɗin gwiwar, musamman yadda za a warware batun wanda zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa.

Atiku zai lashe jihohin Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin dan takarar shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, zai samu nasara a jihohi 13 na yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma a zaben shekarar 2027.

Amaechi ya kuma yi hasashen cewa ADC za ta lashe jihohin Neja, Kogi da Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya, yayin da ya dage cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha wahala wajen samun kuri’u a wasu yankunan kasar. R

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng