'Ku Duba Darajar Mahaifinsa': Gwamna Ya Nema wa Yusuf Buhari Alfarma a 2027

'Ku Duba Darajar Mahaifinsa': Gwamna Ya Nema wa Yusuf Buhari Alfarma a 2027

  • Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya nemi al’ummar mazabar Daura, Sandamu da Mai’Adua su mara wa Yusuf Buhari baya a zaben 2027
  • Radda ya bayyana Yusuf a matsayin dansu, mai sarauta da kuma uba, inda ya bukaci al’umma su yi la’akari da tarihinsa
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan raya kasa 1,019 a yankin Daura, ciki har da 131 a karamar hukumar Baure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nemi al’ummar mazabar tarayya ta Daura, Sandamu da Mai’Adua su yi la’akari da takarar Yusuf Buhari, dan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a zaben 2027.

Radda ya bukaci mazauna yankin su goyi bayan Yusuf Buhari domin ya wakilce su a majalisar wakilai ta tarayya, tare da sauran 'yan takarar jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

Radda ya roƙi alfarmar zaɓen Yusuf Buhari
Dan marigayi tsohon shugaban kasa a Najeriya, Yusuf Buhari. Hoto: Yusuf Buhari.
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga magoya bayan APC a wani gangamin yakin neman zaben Tinubu/Dikko na 2027 da aka gudanar a makarantar firamare ta Baure I, da ke karamar hukumar Baure ta Katsina, cewar Daily Trust.

Abin da Radda ya ce kan takarar Yusuf Buhari

A yayin jawabinsa, gwamnan ya bayyana Yusuf Buhari a matsayin dan yankin, mai sarauta da kuma uba, yana mai kira ga al’umma da su yi la’akari da asalinsa da irin rawar da zai iya takawa wajen wakiltar mazabarsu.

Ya kuma bukaci masu kada kuri’a su marawa dan takarar APC na kujerar sanata mai wakiltar shiyyar Daura baya, tare da sauran 'yan takarar jam’iyyar.

Radda ya bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta samu nasara a babban zaben 2027, yana mai danganta hakan da ayyukan da gwamnatocin jam’iyyar suka gudanar a matakai daban-daban.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Matar Gwamna Abba na jihar Kano ta nemi saki a kotu, ta fadi dalili

Ya ce:

"Daga abin da na gani zuwa yanzu, APC na da dimbin magoya baya masu karfafa gwiwa kuma za ta lashe babban zaben 2027 daga sama har kasa.

Wannan ya samo asali ne daga nasarorin da gwamnatocinmu suka samu a dukkan matakai."

Radda ya bayyana ayyukan da ya yi

Baya ga batun zabe, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan raya kasa guda 1,019 a yankin sanatan Daura, ya ce daga cikin ayyukan, an gudanar da kusan 131 a karamar hukumar Baure kadai.

A cewarsa, ayyukan sun shafi bangarorin ilimi, kiwon lafiya, tallafawa jama’a, ci gaban al’umma da walwalar jama'a.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da romon dimokuradiyya ga al’ummomin da ke karkara.

Yusuf Buhari ya fara shirin zaben 2027

A baya, an ji cewa dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya fara shiga jama'a domin tallata manufofinsa game da takarar da zai yi a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Zamfara: An sanar da sakamakon zaben fitar da gwanin dan majalisar tarayyar APC

A wani mataki na hada kan jama'a, Yusuf Buhari ya nada Aliyu Haruna Daura a matsayin wanda zai jagoranci hulda da jama'a a kamfen din shi.

Yan Najeriya da dama sun yi martani kan sanarwar da Yusuf Buhari ya fitar, wasu na yaba masa wasu kuma na cewa har yanzu akwai aiki a gabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.