Bill Gates Ya Fadi Hadarin AI zai Haifar a Duniya a Shekaru Masu Zuwa
- Wanda ya kafa Microsoft, Bill Gates, ya yi gargadin cewa zamanin fasahar AI na iya zama daya daga cikin mafi rikitarwa a tarihin dan Adam
- Bill Gates ya ce ayyuka da dama, musamman na 'yan koyo da masu matsakaicin gogewa, na iya bacewa har abada saboda AI
- Ya bayyana damuwa cewa gwamnatoci da sauran shugabanni ba su shirya yadda ya kamata domin tunkarar matsalolin da AI za ta haifar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Hamshakin attajirin nan kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya yi gargadin cewa sauyin da fasahar AI za ta kawo na iya zama daya daga cikin mafi rikitarwa a tarihin dan Adam.
Gates ya ce fasahar AI na iya taimakawa wajen rage rashin daidaito tsakanin masu arziki da talakawa, ko kuma ta kara fadada gibi tsakaninsu, gwargwadon yadda gwamnatoci da al'umma suka tunkari sauyin.

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa Gates ya bayyana hakan ne a cikin wani dogon rubutu mai taken, “The turbulent AI era is here. The choices we make now are critical,” da ya wallafa a shafinsa na Gates Notes ranar Laraba.
Gargadin Bill Gates kan AI
Bill Gates ya ce duniya ba ta shirya yadda ya kamata domin sauye-sauyen da AI za ta haifar ba, yana mai cewa shugabanni da masana ba su fahimci girman kalubalen da ke gabansu sosai ba.
Ya ce:
"Abin takaici, a yanzu ba mu shirya domin hakan ba. Ban ga wata alama da ke nuna cewa shugabanni, masana da al'ummomi suna fuskantar wadannan kalubale yadda ya kamata ba."
Gates ya ce babban bambanci tsakanin AI da sauran sauye-sauyen fasaha na baya shi ne saurin da za a iya amfani da ita.
A cewarsa, lokacin da kwamfutoci suka fara yaduwa, an shafe shekaru wajen samar da manhajoji, rage farashinsu da kuma koyawa mutane yadda za su yi amfani da su.
Batun rasa sana'o'i da dama
Bill Gates ya bayyana cewa daya daga cikin manyan hadurran da AI za ta iya haifarwa shi ne bacewar ayyukan yi da dama.
New York Times ta wallafa cewa ya ce:
"Za a rasa ayyuka da dama."
Gates ya kara da cewa wasu daga cikin sabbin ayyukan da AI za ta samar za su bukaci kwarewar da za ta iya daukar shekaru kafin mutum ya samu.
Ya ce ayyukan tallace-tallace, kula da kwastomomi, aikin manhajar kwamfuta da aikin masu taimaka wa lauyoyi na daga cikin ayyukan da za su iya fara fuskantar tasirin AI.

Source: Getty Images
AI za ta iya maye ma'aikatatu
Hamshakin attajirin ya ce tasirin AI ba zai tsaya kan ayyukan fasaha kawai ba, domin tana iya fara gudanar da ayyuka irin su tantance masu neman lamuni, nazarin bayanai da kuma taimakawa wajen rarrabe marasa lafiya.
Gates ya ce yayin da fasahar mutum-mutumi ke kara bunkasa, mutum mutumi masu amfani da AI za su iya fara gogayya da mutane wajen wasu ayyukan jiki.
A cewarsa, zuwa karshen wannan shekarun goma, mutum mutumi masu basira na iya fara yin gogayya da mutane a ayyuka irin na gine-gine da bangaren karbar baki.
Ya ce kamfanoni za su iya kara rungumar AI domin rage kashe kudi, wanda zai iya haifar da karancin ayyukan yi masu kyau idan ba a dauki matakin da ya dace ba.
Matasa za su fi fuskantar kalubale
Bill Gates ya ce ya fi damuwa da matasa da ke shirin neman aiki, domin suna iya samun kansu a lokacin da ayyuka suka ragu.
Ya ce babban sauyi zai zo ne idan AI ta kai matsayin da za ta iya gudanar da ayyuka da kusan babu kuskure ba tare da bukatar mutum ya rika duba ta ba.
A cewarsa, idan hakan ta faru, kamfanoni za su samu dalilin tattalin arziki na barin AI ta gudanar da wasu ayyukan da a yanzu mutane ke yi.
Amurka ta dakile kutsen China
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumomin tsaron Amurka sun sanar da dakile wani gagarumin shirin kutse ta yanar gizo da aka ce wasu masu kutse masu alaka da gwamnatin China suka gudanar na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan
Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano
Ma'aikatar Shari'a da hukumar FBI sun ce sun kwace wasu shafukan intanet guda biyu da ake amfani da su wajen kai hare-hare kan muhimman cibiyoyi da hanyoyin sadarwa.
Rahotanni sun ce masu kutse sun kai hari ko kuma sun yi yunkurin kutsawa cikin cibiyoyi irin su NASA, babban bankin Amurka, Ma'aikatar Makamashi da sauran muhimman hukumomi.
Asali: Legit.ng


