'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace Wasu a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace Wasu a Sokoto

  • ’Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da sace wasu mazauna garin Yartsakuwa da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto
  • Maharan sun kuma kwashe dabbobi yayin harin da suka kai da sanyin safiyar Lahadi kamar yadda rahotanni suka bayyana
  • Wani wanda ya tsira ya ce an sace ’yar uwarsa da matan ’yan uwansa guda huɗu a harin da ya jefa mazauna cikin zulumi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Sokoto - ’Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mazauna garin Yartsakuwa da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto

Kara karanta wannan

Sama da mutum 50 sun mutu da yan sa kai suka yi arangama da wasu yan bindiga

Maharan sun kuma kwashe dabbobi yayin harin da suka kai wa al’ummar garin da sanyin safiyar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2026.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch ta WhatsApp.

Ya ce mutane uku ne aka kashe, yayin da aka sace wasu mazauna garin tare da kwashe dabbobi.

Yadda aka yi barna a jihar Sokoto
Jihar Sokoto, inda aka fi samun tabarbarewar tsaro
Source: Original

Wani jami’in tsaro ma ya tabbatar da harin, inda ya ce maharan sun shiga garin tare da kashe mutane uku kafin su yi awon gaba da wasu mazauna da dabbobi.

Mutum ya ba da labarin harin

Wani wanda ya tsira daga harin mai suna Najeeb Yartsakuwa, ya bayyana cewa maharan sun shiga gidan iyalinsu tare da sace ’yar uwarsa ta cikinsa da matan ’yan uwansa guda huɗu.

Ya kuma ce an sace wasu mata daga cikin al’ummar garin, amma ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Najeeb ya yi ikirarin cewa mutane huɗu ne suka mutu a harin, maza uku da mace ɗaya.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan bindiga sun rutsa 'yan gudun hijira a hanyar zuwa gona

Sai dai adadin da ya bayyana ya bambanta da na rundunar ’yan sandan jihar, wadda ta tabbatar da mutuwar mutane uku.

Najeeb ya bayyana alhininsa kan harin tare da kira ga jama’a da su yi addu’ar Allah ya dawo da mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya.

Matsalar tsaro a Sokoto

Wannan hari ya ƙara jaddada matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu yankunan karkara na jihar Sokoto, inda ake samun hare-hare da satar mutane da kuma kwashe dabbobi.

A watan Satumban 2026, an ruwaito cewa dakarun Operation Fansan Yamma sun kwato garken shanu da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka sace a yankin Kebbe na jihar.

Dakarun sun samu nasarar kwato dabbobin ne bayan samun bayanan sirri kan wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne da ke tserewa da su.

Harin na baya-bayan nan ya sake janyo damuwa kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar yankunan karkara na jihar.

Kara karanta wannan

Abin da ake zargi ya tabbata, jagoran ƴan bindiga ya faɗi dalilansu na ɗaukar makami

Matsalar tsaro a Najeriya

A yankuna daban-daban na kasar nan, ana yawan samun hare-haren 'yan ta'adda tare da neman kudin fansa kafin sakin wadanda suka sace.

Sai dai, an fi samun wadannan hare-hare a Arewacin Najeriya, inda aka hallaka mutane da yawa tare da lalata dukiyoyi da salwatar arziki.

Gwamnatin kasar nan na yawan bayyana aniyar daukar matakai, sai dai abubuwan kara tabarbarewa suke a yankunan Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng