Sanata Yari Ya Taso 'Yan Adawa a Gaba kan Rashin Tsaro, Ya Fadi Matsalar da Suka Samu

Sanata Yari Ya Taso 'Yan Adawa a Gaba kan Rashin Tsaro, Ya Fadi Matsalar da Suka Samu

  • Abdulaziz Yari ya ce waɗanda ke zargin APC da rashin shirin magance matsalar tsaro sun gaza magance matsalar tsawon sama da shekaru 20
  • Ya yi alƙawarin cewa APC za ta aiwatar da dukkan manufofin da ta bayyana a cikin kundin shirinta
  • Sanata Yari ya ce manyan ’yan siyasar Plateau sun tabbatar wa Tinubu cewa jihar za ta ba shi cikakken goyon baya a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Darakta Janar na Kwamitin Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na APC (APC-PCC), Sanata Abdulaziz Yari, ya yi martani ga masu cewa jam'iyyarsu ta gaza magance matsalar rashin tsaro.

Sanata Yari ya zargi waɗanda ke cewa jam’iyyarsu ba ta da shirin magance matsalar tsaro da cewa sun gaza magance matsalar tsawon sama da shekaru 20.

Sanata Yari ya soki 'yan adawa
Sanata Abdulaziz Yari na jawabi a wajen taron APC Hoto: Almansoor Gusau
Source: Facebook

Yari ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Jos, babban birnin jihar Plateau, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsaro ko tazarcen Tinubu: Matawalle ya bayyana babban burinsa a 2027

Me Yari ya ce kan 'yan adawa?

Ya ce waɗanda ke sukar APC kan matsalar tsaro sun kasa ɗaukar matakan magance ta a lokacin da suke mulki, yana mai cewa matsalar ta samo asali ne a lokacin gwamnatocinsu.

A kalamansa:

“Waɗanda ke cewa ba mu da shirin magance matsalar tsaro, ina so na tunatar da su cewa ba su yi komai ba kan matsalar tsaro tsawon sama da shekaru 20, domin matsalar ta fara ne a lokacin mulkinsu.”

APC ta yi alƙawarin cika manufofinta

Sanata Yari ya bayyana cewa APC za ta aiwatar da dukkan manufofin da ta bayyana a cikin kundin shirinta ba tare da kaucewa ba.

Ya yi alƙawarin cewa zuwa shekarar 2031, kusan dukkan abubuwan da jam’iyyar ta yi wa ’yan Najeriya alƙawari za su kasance an cimma su.

Shugaban APC-PCC ya kuma shaida wa mahalarta gangamin cewa manyan ’yan siyasar Plateau sun hallara domin tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa zai samu goyon bayan jihar a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jigo a ADC ya gano abin da Tinubu ke fargaba kan zaben 2027

“Manyan ’yan siyasar Plateau da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar jihar suna nan a gabanku domin tabbatar muku cewa a zaɓen 2027, Plateau ta tabbatar da samun ƙuri’u 101%.”

Yari ya yaba wa Tinubu kan kuɗaɗen asusun tarayya

Yari ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya ce kuɗaɗen da ke cikin asusun tarayya suka ƙaru tun bayan hawansa mulki.

Ya bayyana cewa a watan Yunin 2023, lokacin da Tinubu ya karɓi mulki, asusun tarayya yana da Naira biliyan 732.

Sai dai tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce a halin yanzu ana ƙirga kuɗaɗen asusun ne da tiriliyoyin Naira.

“Shi ne mutumin da ya tarar da asusun tarayyar Najeriya a watan Yunin 2023 yana da Naira biliyan 732. Amma a yau, muna gode wa Allah, Mai girma Shugaban Ƙasa, muna gode maka bisa ƙoƙarinka da salon shugabancinka na musamman. Yanzu muna ƙirga kuɗaɗen asusun tarayya da tiriliyoyin Naira.” In ji shi.
Sanata Yari ya yi maganar rashin tsaro
Sanata Abdulaziz Yari a wajen taron APC a Plateau Hoto: Almansoor Gusau
Source: Facebook

Yari ya magantu kan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abdulaziz Yari, daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya bugi kirji kan tasirin Arewa a zabe.

Ya bayyana cewa Arewa za ta samar wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u fiye da dukkan yankin Kudu maso Yamma a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng