Gwamna Radda Ya Waiwayi Sarakuna, Ya Yi Masu Babban Tagomashi a Katsina

Gwamna Radda Ya Waiwayi Sarakuna, Ya Yi Masu Babban Tagomashi a Katsina

  • Gwamna Dikko Radda ya umarci a biya duk kuɗaɗen da sarakunan gargajiya ke bin gwamnati a jihar Katsina ba tare da ƙarin jinkiri ba
  • Gwamnan ya bukaci sarakunan da ke fuskantar matsalar jinkirin biyan haƙƙoƙinsu su kai ƙorafinsu kai tsaye ofishinsa
  • Dikko Umaru Radda ya kuma yi alƙawarin tallafa wa gyaran masallacin da ba a kammala ginawa ba, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen magance matsalar tsaro da bunƙasa al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayar da umarnin gaggauta biyan duk haƙƙoƙin kuɗi da ake bin sarakunan gargajiya a faɗin jihar.

Radda ya bayar da umarnin ne ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026 yayin ganawa da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da wakilan al’umma a fadar Hakimin gundumar Baure.

Radda ya yi gata ga sarakuna
Gwamna Dikko Umaru Radda na jawabi a wajen taro Hoto: Mustapha Samaila Ingawa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron na daga cikin rangadin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko/Jobe a shiyyar Daura.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fadi halin Peter Obi da ya bambanta shi da saura

Radda ya nemi a biya sarakuna haƙƙoƙinsu

Gwamnan ya ce bai kamata a yi watsi da duk wani mai riƙe da sarautar gargajiya da ya cancanci samun irin waɗannan kuɗaɗe ba.

Ya kuma buƙaci sarakunan da ke fuskantar jinkirin biyan haƙƙoƙinsu da su kai ƙorafinsu kai tsaye ofishinsa, tare da gabatar da cikakkun bayanai domin ɗaukar matakin gaggawa.

A kalamansa, Radda ya ce:

“Ina kallon ku a matsayin iyayena, ni kuma ɗanku ne. Na zo nan ne domin girmama ku da kuma nuna godiyata bisa addu’o’inku, shawarwarinku da goyon bayan da kuke ba ni.”

Gwamnan zai tallafa wa gyaran masallaci

Radda ya kuma yi alƙawarin bayar da gudummawa daga kuɗaɗen aljihunsa domin tallafa wa aikin gyaran wani masallaci da ba a kammala ba a yankin.

Ya ɗauki wannan matakin ne bayan shugabannin al’umma sun gabatar masa da roƙon a taimaka wajen kammala aikin.

Gwamnan ya tuna cewa Baure na cikin al’ummomin da ya fara kamfen ɗinsa a shekarar 2023, yana mai cewa dawowarsa yankin na da nasaba da cika alƙawarin nuna godiya ga mutanen da suka mara masa baya.

Kara karanta wannan

Akwai kura: An taso Tinubu a gaba kan yunkurin kinkimo bashin N11trn

Radda ya yi magana kan tsaro

Gwamnan ya yaba wa mazauna yankin bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa cikin lumana.

Ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da aiki tare da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da sauran al’ummomi domin magance matsalar tsaro, tabbatar da zaman lafiya da kuma hanzarta ci gaba.

Gwamnan ya bayyana cewa an ƙirƙiri shirin raya al’umma (Community Development Programme – CDP) ne domin bai wa al’ummomi damar gano tare da tsara ayyukan da suka fi buƙata.

A cewarsa, wannan tsari zai taimaka wajen tabbatar da cewa ayyukan raya ƙasa sun dace da buƙatu da abubuwan da al’umma suka fi ba muhimmanci.

Ya tuna da gudummawar marigayi Buhari

Radda ya kuma amince da irin gudummawar da tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari, ya bayar wajen ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ayyukan alheri da Buhari ya bari a matsayin gadonsa, tare da ƙara inganta jin daɗin mazauna jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Dalung ya hango matsalar da za ta iya zama hatsari ga ADC a zaben 2027

Radda ya umarci a ba sarakuna hakkokinsu
Gwamna Radda na magana a wajen kamfen din APC Hoto: Mustapha Samaila Ingawa
Source: Facebook

Gwamna Radda ya yi kora a gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sallamar shugaban gidan talabijin na jihar, Katsina State Television (KTTV), Malam Abba Zayyan.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne bisa zargin cewa manajan ya kasa tafiyar da tashar yadda ya dace da manufofin gwamnatinsa, duk da makudan kuɗin da aka zuba wajen inganta ayyukanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng