Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Martani Kan Rahoton Kai Wa Tawagar Tinubu Hari

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Martani Kan Rahoton Kai Wa Tawagar Tinubu Hari

  • Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan harkokin sadarwa ta zamani, O’tega Ogra, ya musanta rahotannin cewa wasu matasa sun kai hari kan tawagar shugaban kasar a Abuja.
  • Ogra ya bayyana bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin wanda aka yi amfani da shi wajen yada bayanan da ba su dace da gaskiya ba.
  • Ya wallafa wani bidiyo da ya nuna yadda Tinubu ya fita daga babban masallacin Shehu Shagari bayan idar da sallar Juma’a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fadar shugaban kasa ta yi martani kan rahotannin da ke cewa wasu matasa sun kai hari kan tawagar Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan ya halarci sallar Juma’a a babban masallacin Shehu Shagari da ke Area 1, Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi 'yan siyasa bayan kai wa Pantami da 'yan NDC hari

Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin sadarwa ta zamani, dabarun sadarwa da sabbin kafafen yada labarai, O’tega Ogra, ya musanta rahoton, yana mai cewa bidiyon da ake yadawa a intanet na iya yaudarar jama'a.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da 'yan APC a wajen kamfen. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa ce-ce-ku-cen ya biyo bayan wani bidiyo da jigon jam'iyyar ADC, Dino Melaye, ya wallafa, wanda ya nuna wasu matasa suna jifan wata tawaga da ake zargin ta shugaban kasa ce.

Bayanin fadar shugaban kasa

A cikin bidiyon da Melaye ya wallafa, an ga wasu matasa suna jifan ayarin motocin, yayin da wasu ke rera kalaman “Ba mu yi, ba ma so”.

Wadannan kalamai na Hausa na nufin nuna rashin goyon baya ko kin amincewa da wani mutum ko mataki.

Sai dai Ogra ya mayar da martani a shafinsa na X a ranar Juma’a, inda ya wallafa wani bidiyo da ya nuna Tinubu yana barin masallacin bayan idar da sallar Juma’a.

Ya rubuta cewa:

“Sabanin labarin da 'yan adawa ke kokarin yadawa, tare da bidiyoyin wasu da suke zargin 'yan daba ne da aka biya domin yin hakan a babban masallacin kasa a yau, ga hoton bidiyon shugaban kasa yana barin masallacin bayan sallar Juma’a a wannan rana.”

Kara karanta wannan

An yi wa Tinubu ihun 'ba ma yi' da ya je masallacin Juma'a a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a Makkah. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Karin bayanin fadar shugaban kasa

Bidiyon da Ogra ya wallafa ya nuna shugaba Tinubu sanye da fararen kaya da bakar hula mai alamomin da ya saba amfani da su.

An ga shugaban kasar yana gaisawa da wasu magoya bayansa da suka fito domin tarbarsa, yayin da wasu ke daukar hotunansa kafin ya shiga motar da yake amfani da ita.

Rahotannin da suka saba wa juna sun jawo muhawara a kafafen sada zumunta, yayin da fadar shugaban kasa ke musanta cewa an kai wa Tinubu hari a lokacin ziyararsa masallacin.

Bayanin Sule Lamido kan 2027

A wani labarin, kun ji cewa Sule Lamido, ya ce rashin hadin kan Atiku Abubakar da Peter Obi na kara wa jam'iyyar APC mai mulki damar samun nasara a zaben 2027.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata hira a ranar Juma’a, inda ya tattauna kan zaben 2027 da burin manyan 'yan takarar shugaban kasa.

Ya ce manyan 'yan siyasar kasar sun fi mayar da hankali kan neman mulki maimakon magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng