Bill Gates zai sullubo daga #4 zuwa #17 a jerin Attajiran Duniya a dalilin sakin Mai dakinsa

Bill Gates zai sullubo daga #4 zuwa #17 a jerin Attajiran Duniya a dalilin sakin Mai dakinsa

- Bill Gates da Melinda Gates za su kashe aurensu bayan shekaru 27 tare

- Uwar ‘Ya ‘yan Attajirin ta bukaci a ware mata rabin dukiyar Bill Gates

- Mai kudin zai rasa kaso mai yawa daga cikin Dala $120bn da ya mallaka

Jaridar DailyMail ta ce Bill Gates wanda ya kafa kamfanin Microsoft, zai iya sauka daga mutum na hudu a cikin jerin Attajiran Duniya, ya koma na 17.

Mujallar Forbes ta tabbatar da cewa a halin yanzu, Bill Gates shi ne mutum na hudu da ya fi kowa kudi a Duniya, ya mallaki fiye da fam Dala biliyan 124.

Wadanda su ka sha gaban Attajirin Amurkan su ne: Jeff Bezos, Elon Musk da kuma Bernard Arnault.

KU KARANTA: Attajirin Duniya Bill Gates ya saki Mai dakinsa Melinda

Rahotanni sun bayyana cewa matakin da ya dauka na rabuwa da uwargidarsa, Melinda, zai sa Attajirin mai shekara 64 ya sauko daga matsayin da yake kai.

Karar da Melinda ta kai kotu ta na neman a raba aurensu ya nuna cewa ta na neman a raba dukiyarsu. Da alamun wannan zai sa Mista Bill Gates ya yi kasa.

Alkalai za su fara sauraron karar kashe auren mai shekara 27, ana sa ran za a karkare shari’ar a 2022.

Bill Gates ya kafa kamfanin Microsoft tare da Paul Allen a shekarar 1975, hakan ta sa ya zama matashin da ba a taba jin labarin mai irin kudinsa a Duniya ba.

KU KARANTA: Bill Gates ya fadi kudin da zai bar wa Magada

Bill Gates zai sullubo daga #4 zuwa #17 a jerin Attajiran Duniya a dalilin sakin Mai dakinsa
Bill Gates Hoto: www.dw.com/en
Asali: Getty Images

Sai shekaru fiye da 20 bayan ya samar da wannan kamfani, Gates ya hadu da sahibarsa, Miss Melinda French, su ka yi aure kuma har ta haifa masa ‘ya ‘ya uku.

Ana hasashen cewa irin wannan zai sa Bill Gates ya sauko daga sahun goman farko na masu kudin Duniya, inda Melinda kuma za ta tashi da kudi masu tarin yawa.

A 2019 takwaran Bill Gates, shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya saki mai dakinsa, MacKenzie. Hakan ta sa ya yi asarar 25% na dukiyar da su ka tara.

Idan za ku tuna fitaccen attajirin da MacKenzie Bezos sun amince su sauwake wa junan su. Ana sa ran ta samu N12.5trn a matsayin hasafi na rabuwa daga dukiyarsa.

Bezos bayan ya auri Matarsa ne a shekarar 1993, kuma sun samu 'ya'ya hudu a shekaru 26.

Asali: Legit.ng

Online view pixel