Bayan Yi wa Shugaban INEC Ihu a London, Babbar Matsala Ta Tunkaro Hukumar
- SERAP ta bai wa hukumar INEC wa’adin kwanaki bakwai ta karɓi bayanan binciken ’yan sanda kan rikice-rikicen siyasa da suka faru a ƙasar nan
- Ƙungiyar ta buƙaci shugaban INEC, Joash Amupitan, ya tabbatar da gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a hare-haren idan akwai isassun hujjoji
- SERAP ta yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan INEC idan ta gaza ɗaukar matakin da ya dace kafin cikar wa’adin da aka bayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
ABUJA – Ƙungiyar da ke fafutukar kare haƙƙin jama'a da tabbatar da riƙon amana a Najeriya (SERAP) ta ba hukumar INEC wa'adi kan rikici a kamfen 2027.
SERAP ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gaggauta ɗaukar mataki kan rikice-rikicen siyasa da ke faruwa a sassan ƙasar nan.

Source: Facebook
SERAP ta bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 14 ga Nuwamba, 2026, wadda mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu wanda ta wallafa a X
SERAP ta ba INEC wa'adin mako 1
Ƙungiyar ta bai wa hukumar wa’adin kwanaki bakwai domin ta karɓo bayanan bincike daga rundunar ’yan sanda kan mutanen da aka kama bisa zargin hannu a tashe-tashen hankulan siyasa tun bayan fara kamfen ɗin zaɓen 2027.
A cikin wasiƙar da aka fitar ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba, ƙungiyar ta buƙaci shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifin karya dokokin zaɓe.
Bukatar SERAP ga Hukumar INEC
Ƙungiyar ta buƙaci Amupitan ya umarci lauyoyin hukumar ko waɗanda ta ɗauka domin gudanar da ayyukan shari'a su duba bayanan binciken da 'yan sanda suka tattara.
SERAP ta ce ya kamata a gurfanar da mutanen da aka kama idan binciken da aka gudanar ya nuna akwai hujjojin da za su tabbatar da laifin da suka aikata ƙarƙashin dokar zaɓe ta 2026.
Haka kuma, ta buƙaci hukumar ta matsa wa ’yan sanda lamba domin su faɗaɗa bincike, gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a rikice-rikicen tare da kama waɗanda suka ɗauki nauyin aikata laifukan.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumar INEC ta yi amfani da ikon da sashe na 83 na dokar zaɓe ta 2026 ya ba ta wajen neman bayanin jam’iyyun siyasa da ake zargi da ƙarfafa ko hannu a ayyukan da doka ta haramta.
Ta ce ya kamata hukumar ta hukunta jam’iyyar siyasar da ta ƙi amsa umarnin da ta bayar ta hanyar sanya mata tarar da doka ta tanada.

Source: Facebook
Jerin hare-haren siyasa da SERAP ta bayyana
SERAP ta ce ta damu matuƙa da yawaitar hare-haren siyasa tun bayan fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a ranar 19 ga Agusta, 2026.
Daga cikin abubuwan da ta lissafa akwai zargin hana tawagar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, wucewa a jihar Benue ranar 8 ga Satumba.
Haka kuma, ta ambaci hare-haren da aka kai wa taron jam’iyyar NDC da gangamin PDP a jihar Enugu ranar 12 ga Satumba, da kuma farmakin da aka kai wa tawagar ɗan takarar sanatan ADC, Herberta Okonofua, a jihar Edo ranar 6 ga Oktoba.
INEC ta musanta murabus din Amupitan
Mun ba ku labarin cewa hukumar zaɓe ta INEC ta ce rahoton da ke cewa shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, zai yi murabus ƙarya ne kuma an ƙirƙire shi.
Hukumar ta buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da labarin tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba.
Masu zanga-zanga sun fuskanci Amupitan a wajen Chatham House ranar Alhamis, suna neman ya yi murabus.
Asali: Legit.ng


