Yadda Masu Bincike Za Su Nemi Tallafin Gwamnatin Tarayya a 2026

Yadda Masu Bincike Za Su Nemi Tallafin Gwamnatin Tarayya a 2026

  • Gwamnatin Tarayya ta hannun PTDF ta gayyaci ’yan Najeriya masu bincike da su nemi tallafin ayyukan binciken man fetur da iskar gas na shekarar 2026
  • Shirin ya ƙunshi fannoni takwas da suka haɗa da makamashi, fasahar zamani, kare muhalli da tattalin arzikin man fetur
  • Waɗanda suka cancanta za su iya gabatar da takardun neman tallafin ta intanet kafin ranar 10 ga Fabrairu, 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamnatin Tarayya ta buɗe shirin tallafin binciken man fetur da iskar gas na shekarar 2026, inda ta gayyaci masu bincike ’yan Najeriya da su gabatar da ayyukan da za su taimaka wajen magance ƙalubalen da masana'antar man fetur da iskar gas ke fuskanta a ƙasar.

Asusun Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF) ne ya sanar da shirin, inda ya bayyana cewa manufarsa ita ce ƙarfafa bincike a cikin gida da kuma samar da hanyoyin fasaha na magance matsalolin da ke addabar ɓangaren man fetur.

A cikin sanarwar neman takardun bincike da PTDF ta wallafa ranar 13 ga Nuwamba, 2026, asusun ya ce waɗanda aka zaɓa za su samu tallafin kuɗi a matakai daban-daban bisa cikar manufofin da aka tsara wa ayyukansu.

Kara karanta wannan

Abin da mutane ke cewa bayan sun samu tallafin N50,000 daga Gwamnatin tarayya

Za a bai wa 'yan Najeriya tallafin PTDF
Yadda ake cike takardar tallafin PTDF | Hoto: ptdf.gov.ng/GettyImages
Source: UGC

Waɗanne ne za su iya nema?

A cewar PTDF, masu neman tallafin dole ne su cika wasu sharuɗɗa kafin su cancanci shiga shirin.

Waɗannan sharuɗɗan sun haɗa da:

  • Dole ne mai neman tallafin ya kasance ɗan Najeriya da ke zaune a cikin ƙasar.
  • Ya kasance yana aiki a jami'a, kamfani, cibiyar bincike ko ƙungiya mai zaman kanta.
  • Babban mai jagorantar bincike (Principal Researcher) dole ne ya kasance babban malami.
  • Dole ne babban mai bincike ya kasance a Najeriya, duk da cewa ana iya haɗa ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje cikin tawagar binciken.
  • Ana ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu bincike da ƙwararrun masana'antar man fetur.
  • Haka kuma, PTDF na ƙarfafa haɗin gwiwar masu bincike daga fannoni daban-daban.

Fannonin bincike takwas

PTDF ta bayyana cewa shirin na shekarar 2026 ya ƙunshi manyan fannoni takwas da masu neman tallafin za su iya zaɓa.

Ga fannonin:

1. Tsaron makamashi: Ya ƙunshi bincike kan hanyoyin inganta samar da makamashi, amfani da fasahar AI wajen nazarin albarkatun ƙasa da gano wuraren da ake iya samun man fetur.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta faɗi yankuna da jihohin da su ci moriyar tallafin N50,000

2. Inganta samar da man fetur: Ya shafi sabbin hanyoyin haɓaka samar da mai, kula da bututun mai da rage lalacewar kayayyakin aiki.

3. Amfani da iskar gas: Ya ƙunshi samar da wutar lantarki daga gas, sarrafa iskar gas da rage ƙone ta a wuraren haƙar mai.

4. Sabbin fasahohi da makamashi mai tsafta: Ya haɗa da makamashin rana, iska, adana makamashi da sauran hanyoyin rage gurɓatar muhalli.

5. Kare muhalli: Ya shafi magance malalar mai, sarrafa shara, rage gurɓatar muhalli da kare halittu.

6. Fasahar zamani: Ya ƙunshi amfani da basirar AI, na'urori masu sarrafa kansu, fasahar zamani wajen sa ido kan ayyukan haƙar mai da tsaron bayanai.

7. Injiniyanci da kayayyakin more rayuwa: Ya shafi inganta kayan aikin masana'antar man fetur, ƙera kayayyaki a cikin gida da rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.

8. Tattalin arzikin makamashi: Ya ƙunshi bincike kan farashin mai, manufofin tattalin arziki, kuɗaɗen zuba jari da bunƙasa ƙwarewar ma'aikata.

Yadda ake neman tallafin

Kara karanta wannan

Yadda masu bankin Wema za su duba cancantar samun tallafin N50,000

PTDF ta ce dukkan tsarin neman tallafin zai gudana ne ta intanet.

Masu sha'awar neman tallafin za su iya bin waɗannan matakai:

  1. Su shiga shafin neman tallafin na PTDF ta adireshin https://oilandgasresearch.ptdf.gov.ng.
  2. Su buɗe asusu domin fara neman tallafin.
  3. Su zaɓi fannin binciken da ya dace da aikin da suke son gudanarwa.
  4. Su tsara takardar bincikensu bisa ƙa'idojin da PTDF ta tanada.
  5. Su tabbatar da cewa takardar ta cika dukkan sharuɗɗan da aka gindaya.
  6. Su gabatar da takardar ta hanyar shafin intanet ɗin.

Ƙa'idojin gabatar da takarda

PTDF ta ce takardar bincike ba za ta wuce kalmomi 5,000 ba. Dole ne ta ƙunshi taƙaitaccen bayani, matsalar da ake son magancewa, nazarin binciken da aka gudanar a baya, manufofin aikin da kuma hanyoyin gudanar da binciken.

Sauran abubuwan da ake buƙata sun haɗa da jadawalin gudanar da aikin, tsarin amfani da sakamakon binciken, kasafin kuɗi, hanyoyin horar da masu bincike da jerin majiyoyin bayanai.

Dole ne a rubuta takardar da salon Times New Roman, girman haruffa 12, da tazarar layi 1.5. Haka kuma, dole ne a yi amfani da APA 7 wajen ambaton majiyoyin bayanai.

Kara karanta wannan

Tallafin 50,000: Hanyoyi 6 da masu MoMo za su bi domin duba ko sun cancanta

PTDF ta kuma gargaɗi masu nema da kada su saka sunayensu ko tambarin cibiyoyinsu a cikin takardun binciken da za su gabatar.

Yaushe ne ranar karshe?

Ranar ƙarshe ta gabatar da takardun neman tallafin ita ce Laraba, 10 ga Fabrairu, 2027.

Masu neman tallafin na iya sa ido kan shafin PTDF da hanyoyin sadarwarsu domin samun bayanai kan tantance takardunsu, gayyatar waɗanda aka zaɓa da sauran matakan shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng