Sama da Mutum 50 Sun Mutu da Yan Sa Kai Suka Yi Arangama da Wasu Yan Bindiga

Sama da Mutum 50 Sun Mutu da Yan Sa Kai Suka Yi Arangama da Wasu Yan Bindiga

  • Sama da mutane 40 sun mutu yayin wata rangama mai zafi tsskanin ’yan bindiga da ’yan sa-kai a jihar Zamfara
  • An ce an kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga mai suna Jijji, wanda ya jagoranci sace wasu mutane da dama a jihar
  • Mazauna yankin sun bukaci gwamnati ta samar wa ’yan sa-kai bindigogi da alburusai domin yakar ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Arangama tsakanin ’yan bindiga da ’yan sa-kai ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 50 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda mazauna yankin suka shaida.

Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da hare-haren kungiyoyin masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da masu satar shanu suka addaba.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfra da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Vangaurd ta rahoto cewa ƙungiyoyin na kai hare-hare kan kauyuka, kashewa da sace mazauna yankunan, tare da kwashe kayayyaki daga gidaje kafin su cinna musu wuta.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan bindiga sun rutsa 'yan gudun hijira a hanyar zuwa gona

Yan sa-kai sun gwabzz da yan bindiga

Majiyoyi sun ce ’yan sa-kai daga kauyen Zoma da ke karamar hukumar Bukkuyum sun yi wa ’yan bindigar kwanton-bauna ne a ranar Alhamis, yayin da suke wucewa ta kauyen bayan sun sato mutane a karamar hukumar Gummi.

Dagacin kauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce:

“An sanar da mu cewa ’yan bindigar na dosowa inda muke, don haka ’yan sa-kai suka yi musu kwanton-bauna, suka kuma fafata da su a mummunan musayar wuta. Sun kashe ’yan bindiga 44 mu kuma mun rasa jami'ai tara a fadan,” in ji dagacin.

Basarken ya kara da cewa an kuma kashe wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga mai suna Jijji, wanda ya jagoranci sace mutanen.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ya ce rundunar ba ta samu cikakken bayani kan arangamar ba tukuna.

An bukaci gwamnati da inganta yan sa-kai

Mazauna kauyen Zoma, Kabiru Tafida da Basiru Buhari, sun ba da irin wannan bayani kan rikicin da kuma adadin wadanda suka mutu.

Kara karanta wannan

Abin da ake zargi ya tabbata, jagoran ƴan bindiga ya faɗi dalilansu na ɗaukar makami

Wani mai suna Buhari ya ce:

“Muna kira ga hukumomi da su samar wa ’yan banga bindigogi da alburusai domin yakar wadannan ’yan bindiga da ke amfani da manyan makamai.”
Daud Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a wurin kaddamar da rundunar tsaron al'umma Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ta’addancin ’yan bindiga a Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a Afirka, ya samo asali ne daga rikice-rikicen da ke tsakanin makiyaya da manoma kan filaye da ruwa.

Tabarbarewar tsaro da tsadar rayuwa sun zama manyan batutuwan da ke jan hankali a yakin neman zaben shugaban kasa da ake yi, yayin da Bola Tinubu ke neman wa’adi na biyu a zaben watan Janairu, 2026.

Yan bindiga sun ƙona yan gida daya

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun kashe mutane 12 a iyali guda bayan sun cinna wa ɗakin da suka ɓuya wuta a Jihar Zamfara.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Sanusi Ahmed Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin imani.

Baya ga kashe mutane 12, maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mazauna ƙauyen, amma har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka tafi da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262