Bayan Kusan Shekaru 10, Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Kuskuren da Buhari Ya Yi
- Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta ce nada Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC ya saɓa doka
- Kotun ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya amince da ci gaba da riƙe Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar
- Magu ya kasance mukaddashin shugaban EFCC daga 2015 zuwa watan Yulin 2020, lokacin da aka dakatar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa tsawaita zaman Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ya saɓa doka.
Kotun ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta amince da tsawaita wa'adin Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC, wanda gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ta yi.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙarar ne ya yanke hukuncin ranar Litinin a kan ƙarar da wani lauya, Johnmary Jideobi, ya shigar.
Jideobi ya ƙalubalanci ci gaba da zaman Magu a mukamin bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa a matsayin cikakken shugaban EFCC sau biyu.
Ƙarar ta samo asali ne daga hukuncin da Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar 4 ga Disamba, 2019.
Magu ya kasance mukaddashin shugaban EFCC daga shekarar 2015 har zuwa Yulin 2020, lokacin da aka dakatar da shi daga mukamin.
Yadda lauya ya kai kara gaban kotu
Jideobi ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya a watan Maris na 2017, yana mai cewa Magu ba zai iya ci gaba da kasancewa mukaddashin shugaban EFCC ba bayan Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa.
A hukuncin da ta yanke a shekarar 2019, alkalin ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar ci gaba da zaman Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC.

Kara karanta wannan
Ma'aikatan gwamnatin Najeriya sun ji wuta, sun tura wasiƙa mai zafi ga Shugaba Tinubu
Ta ce dokar EFCC, musamman sashe na 2(3), ba ta takaita ikon shugaban ƙasa na ci gaba da riƙe Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar ba.
Lauya ya daukaka kara
Sai dai Jideobi bai gamsu da hukuncin ba, inda ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Ya kafa hujjar cewa shugaban EFCC yana da wa’adin shekaru huɗu, wanda za a iya sabunta shi sau ɗaya, kuma Magu ya wuce lokacin da doka ta tanada ba tare da amincewar Majalisar Dattawa ba.

Source: Facebook
Ya kuma yi zargin cewa naɗin Magu a matsayin mukaddashi ya ƙare ta hanyar aiki da doka bayan Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa.
Jideobi ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya tare da amincewa da buƙatun da ya gabatar a ƙarar tasa ta farko.
EFCC za ta binciki aikin wutar Mambolla
Kun ji cewa EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta kafa wani kwamiti da zai binciki wadanda sunansu ya fito a badakalar akin wutan Mambilla.
Wannan bincike ya biyo bayan nasarar da Najeriya ta samu a kotun ICC a kan kamfanin Sunrise Power, aka yi watsi da neman biyan dalolin kudi.
Asali: Legit.ng
