Kutungwiwar Majalisa: Allah sarki karshen Magu yazo a matsayin shugaban EFCC
- In ka ji ki gudu to sa gudu ne bai zo ba, yanzu haka dai Majalisa ta tirsasa Fadar shugaban kasa amincewa da cire Magu.
- Bayan kiki-kaka da aka sha tsakanin Majalisa da bangaren zartarwa, daya ya bayar da kai bori ya hau
Yanzu haka dai shirye-shirye sun yi nisa tsakanin Majalisa da fadar shugaban kasa na cire shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
Sauya Magun dai ya biyo bayan karin girman da ya samu zuwa mukamin kwamishinan yan sanda.
A wani bayan sirri da jarida Vanguard ta tattara, ya nuna cewa, hakan ya biyo bayan yunkurin daidaita tsattsamar dangantakar da ke akwai tsakanin fadar shugaban kasar da majalisar..
Yanzu da aka kara masa girma, ana sa ran Ibrahim Magun dole zai tafi izuwa kwalejin yan sanda ta kasa dake Kuru a jihar Plateau domin karo karatun mayan jami’an yan sanda.
Majalisar dai ta nuna tirjiya kan amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC har sau biyu, kuma majalisar ce kadai ke da ikon tabbatar da wanda barin zartarwa suka zaba kafin ya zama cikaken halastacce bana na rikon kwarya ba.
KU KARANTA: Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna
Sai dai kuma mai makon barin na zartarwar ya canzo sunan Ibrahim Magu da wani, sai ya bijire, kowa ya ja daga. Majalisar dattijan sunki amincewa da shi haka kuma fadar shugaban kasar taki yarda ta canza waninsa.
Wannan dalili ne ya sanya dangataka tsakanin manyan kafafun gwamnatin Najeriya suka shiga yiwa juna kallon hadarin kaji.
Sakamakon jan daga da fadar shugaban kasar tayi ne na cewa ba sai lallai majalisar ta sahale mata nadin wanda take da bukatar nadawa ne ba, ya sanya jan kafa da yin tafiyar hawainiya ga duk wani kudiri da fadar shugaban kasar ke bukatar amincewar majalisar.
To amma sai dai zamu iya cewa wannan sa toka sa katsi tazo karshe ganin yadda yanzu fadar shugaban kasar ta bada kai bori ya hau na canza Magu daga shugabancin EFCC, domin gyaruwar dangantakar ta su da majalisar. Kamar yadda wani bincike na bayan gafe da jaridar Vanguard ta gudanar ya nuna.
shi dai Ibrahim ba’a fi shekara guda da kara masa girma ba a matsayin mataimakin kwamishinan yan sanda ba, sai gashi kuma yanzu an sake kara masa wani mukamin, wanda hakan ya haifar da tunin tabbas da akwai lauje cikin nadi.
An dai zabi Magu a matsayin shugaban riko na hukumar ta EFCC ne, tun a shekarar 2015 a lokacin yana da mukamin mataimakin kwamishina (II) da tunanin yiwuwar tafiyarsa karo karatu don kara masa girma cikin lokaci kalilan, amma hakan bai samu ba, watakila sakamakon rikon kwaryar hukumar da akai masa.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo na daga cikin wadanda suka daurewa Magu gindi wajen ganin ya cigaba da zama shugaban riko na EFCC duk kuwa da cewa Majalisa taki amincewa da shi.
irin wannan karin girma na jeka da halinka ba yau aka fara shi a hukumar ta EFCC ba, domin bayan tafiyar Obasanjo da Marigayi Umaru Musa ‘YarAdua ya zama shugaban kasa, a lokacin Malam Nuhu Ribado ne shugaban EFCC haka akai masa a 2007.
Magu dai yana da kyakkyawan tahiri na kwarewa wajen yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa da sauran barayin kudin al’umma, musamman yan siyasa, hakan yasa wasu suke ganin shi ne musabbabin dalilin da sanya Majalisar ke tararrabin amincewa da shi a matsayin shugaban EFCC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng