Majalisar Dattawa ta amince da nade-naden Buhari 207 ba tare da ya waiwayi Magu ba

Majalisar Dattawa ta amince da nade-naden Buhari 207 ba tare da ya waiwayi Magu ba

A tsawon shekara guda kenan kawo yanzu, bincike ya nuna cewa majalisar dattawa ta amince da nade-naden shugaba Muhammadu Buhari guda 207 tun bayan kafuwarta.

Cikin nade-naden da majalisar ta amince da su sun hadar da manyan alkalai, ministoci, jakadu, kwamishinoni da kuma shugabannin hukomomi da cibiyoyi gwamnatin tarayya.

Sai dai har kawo yanzu, Buhari bai yi wani waiwaye ba domin tabbatar da nadin mukamin mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu.

Tun a ranar 9 ga watan Nuwamba na shekarar 2015 ne, shugaban Buhari ya zabi Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC tare da neman majalisar dattawa ta amince da nadinsa.

Sai dai gabanin majalisar ta amince da nadin Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa, ya ci gaba da rike mukamin har kawo yanzu.

Har sau biyu majalisar wadda Bukola Saraki ya jagoranta tana kin amincewa da nadin Magu, inda ta yi watsi da shi saboda rahoton da Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta bayar a kansa.

Sai dai duk da hakan Magu ya ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban hukumar ta EFCC biyo bayan zaman doya da manja da aka rika yi tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa.

Majalisar Dattawa; Sanata Ahmad Lawan tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Majalisar Dattawa; Sanata Ahmad Lawan tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Tun bayan kafuwar sabuwar majalisar dattawa ta 9 a tarihi, Buhari ya aike mata da sunayen sama da mutum 200 domin ta amince da nadin mukamansu ba tare da ya aika da na Magu ba.

Wannan na zuwa ne duk da tabbacin da shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya bayar na cewa, majalisarsa za ta amince da nadin Magu cikin hanzari da zarar an aiko mata da sunasa.

A yayin da shugaban kwamitin da ke bai wa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, ya ziyarci zauren majalisar a ranar 21 ga watan Nuwamban 2019, Sanata Lawan ya ce ba a aiko musu da bukatar da tabbatar da nadin Magu ba.

A halin yanzu dai ana sa ran Magu zai yi ritaya daga aikin hukumar 'yan sanda nan da watanni 23 masu zuwa, yayin da zai cika shekaru 60 da haihuwa.

KARANTA KUMA: Likitoci za su janye yajin aiki bayan ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya

Sabuwar majalisar wadda ta ke takama da kyakkyawar alaka tsakaninta da fadar shugaban kasa, ta ki amincewa da nadin mukami daya ne kacal cikin dukkanin nade-naden da Buhari ya yi a tsawon shekaru guda.

Cikin jerin nade-naden da Buhari ya yi wanda majalisar dattawan ta yi hanzarin amincewa da su sun hadar da:

Nadin Alkalin Alkalai na Najeriya; Tanko Muhammad a watan Yulin 2019 da nadin Ministoci 43 a watan Agustan 2019.

Nadin Babban Kwamishinan Hukumar Sadarwa ta Najeriya, Adeleke Adewolu a Satumban 2019 da Shugabanni 15 na Hukumar raya Neja Delta a watan Okotoba na 2019.

Tabbatar da nadin Alkalin Babbar Kotun Najeriya; John Tsoho a Nuwamban 2019 da kuma Ciyamoni da Kwamishinoni 13 na Hukumar Kula da Majalisar Dattawa a Dasumban 2019.

Amincewa da nadin Shugabanni 18 na Hukumar Jin dafin Alhazai ta NAHCON a watan Dasumban 2019.

Haka kuma dai a watan Dasumban na 2019, majalisar ta amince da nadin shugabannin 12 masu kula da Hukumar tara Haraji (FIRS)

Sai kuma a watan na Dasumba dai, majalisar ta amince da Edward Adamu, a matsayin Ciyaman na Hukumar tara kadarorin Najeriya.

A watan Janairun 2020, Buhari ya nemi majalisar da tabbatar da nadin mukamin Kingsley Obiora a matsayin mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya da kuma Nuhu Musa, a matsayin Darakta Janar na Hukumar Kula Da Sufurin Jiragen Sama, NCAA.

Shugaban kasar ya kuma nemi a tabbatar da Adeolu Akande, a matsayin ciyaman na Hukumar Kula da Hukumar Sadarwa ta Kasa, da Uche Onwude a matsayin mamba na reshen Kudu maso Gabas.

A watan Afrilun 2020, shugaba Buhari ya nemi majalisar ta amince da shugabanni 38 na Hukumar Kula da Da'ar Ma'aikata da kuma mutum 7 na Hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya (RMAFC).

Kamar yadda binciken jaridar The Punch ya nuna, majalisar a watan Mayun 2020, ta amince da nadin jakadu 42 da shugaban kasar ya aike mata da sunayensu.

An nada Lamido Yuguda a matsayin babban daraktan Hukumar Tsaro da Canji (SEC) Securities and Exchange Commission a watan Yunin 2020 da wasu Kwamshinonin hukumar uku.

A watan Yunin dai na 2020, majalisar ta amince da nadin Daraktoci biyu na Hukumar kare hakkin masu ajiya a bankuna NDIC da mambobi uku na Hukumar Kula da Shari'a NLRC.

A baya bayan nan ne cikin watan Yuni, majalisar dattawa ta amince da mai shari'a Monica Dongbam-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Sai kuma Darakta Janar na Hukumar Sadarwa NCC, Farfesa Umar Dambatta, da majalisar ta amince bayan shugaba Buhari ya sake sabunta nadin mukaminsa a wa'adi na biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel