Sultan Ya Kausasa Harshe kan Zubar da Jini, Ya Yi Kira ga Tinubu
- Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, ta bukaci gwamnatin Tinubu ta gaggauta kawo karshen zubar da jini a Najeriya
- JNI ta ce hare-hare, kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci na ci gaba da jefa al’ummar Najeriya cikin fargaba da rashin tabbas
- Sultan ya kuma bukaci a sake duba tsarin tsaron Najeriya tare da sauya salo daga martani bayan faruwar hari zuwa amfani da bayanan sirri wajen dakile hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen zubar da jini a sassan Najeriya.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar jiya, Sultan ya yi addu’ar Allah Ya dawo da zaman lafiya a Arewa da sauran sassan Najeriya.

Source: Facebook
Batun sake fasalin tsarin tsaro
Leadership ta wallafa cewa Sultan ya bukaci a sake duba tsarin tsaron Najeriya gaba daya, inda ya ce ya kamata hukumomin tsaro su kara mayar da hankali kan amfani da bayanan sirri wajen hana hare-hare kafin su faru.
Ya ce hakan na bukatar cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi domin hukumomin tsaro su samu damar dakile barazanar tun kafin ta kai ga faruwa.
Ya kuma bukaci a mayar da hankali wajen ganowa tare da tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, da kuma hanyoyin da suke bi wajen samun kayayyakin aikata laifi.
Sultan ya ce dakile hanyoyin da ake bi wajen safarar makamai, alburusai, man fetur, abinci, babura da sauran kayayyakin da ke taimaka wa kungiyoyin masu dauke da makamai yana da matukar muhimmanci.
Batun mutuwar mutane 37 a Niger
Kungiyar ta kuma yi maraba da matakin gwamnatin tarayya na kafa bincike mai zaman kansa kan mutuwar mutane 37 da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Niger.

Kara karanta wannan
Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya
The Nation ta wallafa cewa JNI ta kuma goyi bayan dakatar da jami’an da ke da alaka da lamarin har sai an kammala binciken.
Sai dai kungiyar ta ce lamarin ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci kan yadda aka kama mutanen, yanayin da aka tsare su, samun kulawar lafiya da sauransu.

Source: Facebook
Magana kan hare-hare a jihohi
JNI ta ce bayanan da ta tattara kan hare-hare da kashe-kashe a Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kebbi, Borno, Yobe, Adamawa, Niger, Gombe, Kogi, Benue da Plateau da sauran sassan Najeriya na nuna halin tsaro mai matukar tayar da hankali.
Kungiyar ta ce a Sokoto kadai, hare-haren baya-bayan nan sun haddasa mutuwar mutane, jikkatawa, garkuwa da satar shanu, yayin da sojoji ke ci gaba da gudanar da ayyuka domin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.
Ta ce duk da ayyukan sojoji da sauran jami’an tsaro a wurare daban-daban, ana ci gaba da kashewa da yin garkuwa da mutane a gidajensu da kan manyan hanyoyi, lamarin da ke tilasta wasu barin gidajensu.
Batun 'yan sandan jihohi

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar jihar Osun ta zama ta farko wajen amincewa da kafa rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa su domin ba jihohi damar lura da matsalolin tsaron da ke damunsu kai tsaye.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan sauran jihohin Najeriya 35 domin ganin matakin da za su dauka wajen kafa 'yan sandan domin tabbatar da tsaro.
Asali: Legit.ng
