Wata Sabuwa: Ana Zargin 'Tsoro' Ya Hana Shugaba Tinubu zuwa Taron UNGA a Kasar Amurka

Wata Sabuwa: Ana Zargin 'Tsoro' Ya Hana Shugaba Tinubu zuwa Taron UNGA a Kasar Amurka

  • Kenneth Okonkwo ya yi zargin cewa Shugaba Boka Tinubu na guje wa zuwa Amurka saboda tsoron yiwuwar Trump ya kama shi
  • Mai magagana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar ya danganta rashin halartar taron UNGA DA tsofaffin zarge-zargen da ake wa Tinubu
  • Fadar Shugaban Ƙasa ta ce shari’ar da ake yi kan bayanan Tinubu a Amurka ta shafi bayyana bayanan gwamnati ne, ba shari’ar laifi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na guje wa Amurka ne saboda tsoron yiwuwar Shugaba Donald Trump ya sa a kama shi.

Okonkwo ya yi wannan zargin ne yayin da yake magana kan rashin halartar Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ake gudanarwa a New York.

Kara karanta wannan

'Ba shi da lafiya,' Fasto Ayodele ya yi hasashen rasuwar Tinubu a kan mulki

Kenneth Okonkwo
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo Hoto: Kenneth Okonkwo
Source: Twitter

Hadimin Atiku ya bayyana hasashen sa ne wani shirin Arise News mai suna Prime Time, yayin da ake ta tsokaci kan tura Kashim Shettima ya wakilci Tinubu.

Okonkwo ya ce Tinubu na jin tsoro

Okonkwo ya tambayi dalilin da ya sa Tinubu ya sake kaurace wa taron na shekara-shekara, yana zargin cewa shugaban na guje wa Amurka ne da gangan.

Ya yi zargin cewa Tinubu ba ya son zuwa Amurka ne saboda sake farfaɗowar batutuwan da suka shafi tsofaffin zarge-zargen miyagun ƙwayoyi da bayanan shari’a da suka shafe shi.

“Tinubu yana ɓoye kansa ne, yana gudun kada Trump ya kama shi,” in ji Okonkwo.

Ya kuma ce rashin halartar Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya na ci gaba da zama abin tambaya, yana mai cewa shugaban bai halarci taron da kansa ba tsawon shekaru uku a jere bayan halartar taron na 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gano abin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala bayan cire tallafin fetur

“Me yake yi? Bai je Majalisar Ɗinkin Duniya ba tsawon shekaru uku a jere. Mutum mai hankali zai ce yana ɓoye kansa ne daga Amurka,” in ji Okonkwo.

Okonkwo ya tabo kalaman Jimoh Ibrahim

Tsohon jigon LP ya tabo kalaman da a baya aka danganta wa Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, wanda ya ce Tinubu zai halarci taron tare da zama a sahun gaba kusa da Trump.

“Ku tuna, jakadanmu a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya gaya mana cikin farin ciki cewa shugaban zai zo ya zauna a sahun gaba tare da Shugaba Trump domin ya wakilce mu. Me ya faru? Ƙarya. Shugaban bai je ba,” in ji shi.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Okonkwo ya danganta rashin halartar Tinubu da sabuwar muhawara da ta taso kan bayanan Amurka da suka shafi shugaban, ciki har da batun ƙwace kuɗi kusan dala 460,000 a shekarar 1993.

“Yanzu, ta yaya aka samu wata takarda da shugaban ƙasarku ya shigar yana cewa ba ya son a fitar da bayanansa a Amurka? Ana zargin hakan ya shafi zarginsa da safarar miyagun ƙwayoyi,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya fadi gaskiya, ya ce farashin man fetur zai iya ƙara tsada a Najeriya

Amurka da Najeriya sun kulla yarjejeniya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya da Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin bunƙasa fannin ma’adinan ƙasa a Najeriya.

An rattaba hannun kan yarjejeniyar ne a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda ke gudana a birnin New York na kasarNAmurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262