Badakaloli 5 da ke Wuyan Atiku Abubakar da Tsohuwar Matarsa ‘Yar Kasar Amurka

Badakaloli 5 da ke Wuyan Atiku Abubakar da Tsohuwar Matarsa ‘Yar Kasar Amurka

  • ICC ta gano cewa kamfanin Sunrise Power ya tura $500,000 zuwa asusun Jennifer Douglas domin neman aikin wutar Mambilla
  • Bayan wannan zargin cin hanci, binciken Majalisar Dattawan Amurka ya goga wa Atiku Abubakar kashi a lokacin yana kan mulki
  • Atiku da Jennifer Douglas sun dade suna fuskantar zarge-zargen almundahana da cin rashawa kafin aurensu ya mutu a shekarar 2021

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Kotun ICC ta kama sunan Atiku Abubakar cikin wata badakala da ta shafi aikin samar da wutar lantarki a Mambilla.

Lokacin da gwamnatin Najeriya ta ba kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Limited aikin, Atiku yana Aso Rock.

Ganin abin da ya je ya dawo game da lamarin, Premium Times ta jero wasu kashi akalla biyar da aka goga wa babban ‘dan siyasar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da mai dakinsa a jihar Adamawa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Badakaloli a wuyan Atiku Abubkar da Jennifer Douglas

1. Samun kwangilar aikin Mambilla

Zargin da ake yi shi ne Leno Adesanya na kamfanin Sunrise, ya aika $500, 000 zuwa wani asusun kamfanin Jennifer Douglas a Amurka.

Jennifer Douglas tana cikin matan Atiku sa’ilin da abin ya faru, sai a watan Yunin 2021 suka rabu.

An dade ana zargin Wazirin Adamawa da Douglas da laifuffukan da suka shafi kudi da aka rika tura wa a asirce zuwa kasar wajen.

Ta bude asusu a ketare da sunan Jennifer Douglas Abubakar Family Trust, the Gede Foundation da American University of Nigeria.

Zargin da ake yi shi ne kudin da aka Adesanya ya tura sun yi tasiri wajen samun kwangilar da a karshe sai dai aka kare a kotu.

2. Rashawar kamfanin Siemens

Wata badakala da Atiku Abubakar ya burma ita ce ta kamfanin Siemens. A nan ma dai lambar tsohuwar mai dakinsa sai da ya fito.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya ruguzo kasa bayan Trump da Iran sun fahimci juna

Ana zargin kamfanin na Jamus da yake harkokin sadarwa a biya cin hanci domin samun kwangila a zamanin Olusegun Obansanjo.

Sai da Umaru Yar’Adua ya zama shugaban kasa a samu labarin zargin. An ce kamfanin ya ba jami'ai cin hanci da ya kai $4.5m.

A nan ma an ce an biya kudin ne ta wani asusu da yake da alaka da Jennifer Douglas, sai aka dauko kudin aka dawo da su Najeriya.

An fake da sunan za a yi wani aiki da Siemens saboda kawai a samu kwangilar. A 2008 kamfanin ya biya tarar $1.6bn a Amurka da Jamus.

3. Badakalar Jefferson

A baya hukumomin Amurka sun binciki zargin rashin gaskiya da ke tsakanin ‘dan majalisar kasar, William Jefferson da wasu mutanen Atiku.

Badakalar nan ta shafi wasu kamfanonin Jefferson: iGate, and Netlink Digital Television (NDTV) kamar yadda jaridar FIJ ta taba ruwaitowa.

Da aka shiga kotu a 2008, wani wanda ake shari’a da shi ya amsa cewa sun biya $400,000 domin tallata kamfanin iGate a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda manyan Najeriya da iyalansu 61 suka saye kadarorin $270m a Amurka

Bayanan kotu sun ce Jefferson mai wakiltar mutanen Louisiana a majalisa ya ce ya ba Atiku kudi har $100,000 a matsayincin hanci.

4. Binciken majajalisar Amurka

Wani kwamitin Majalisar dattawan Amurka ya taba yin bincike game da zargin cuwa-cuwar kudi da ake yi da Atiku da Ms Douglas.

Rahoton binciken ya nuna mutanen nan sun yi amfani da wasu asusun bankinsu a kasar Amurka wajen cire kudi sama da $40m.

An sulale da kusan $25m ne ta asusun da aka bude da sunan The Jennifer Douglas Abubakar Family Trust, the Gede Foundation da AUN.

Bankunan sun bude wa matar asusu ne ba tare da sun san cewa ana zarginta da rashin gaskiya ba. PM News ta taba kawo labarin.

5. Takunkumin da aka kakaba wa Atiku

Saboda jerin abubuwan da suka faru ne Gwamnatin Amurka ta rika sa wa tsohon mataimakin shugaban kasar da iyalansa ido.

Wasu bankuna sun shigar a game da Atiku da matasa da yaransa da wasu kamfanonin da ke da alaka da su a gaban hukumar FinCEN.

Kara karanta wannan

Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC

A sanadiyyar haka aka sa ido a kan Atiku, Rukaiyatu, Amina Titi da kamfanonin GTCN da Tanjay. Bayan haka aka hana Atiku bisa.

Da alakarsa da Amurka ta yi tsami, sai Atiku ya koma wa birnin Dubai, a kasar UAE bayan ya saida wasu gidajensa da ke Marlyand.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar tare da matansa wajen kamfe a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kamfanin Amurka zai yi karar Tinubu da FFK

Rahoto ya zo cewa kamfanin Von Batten-Montague-York, na shirin shigar da ƙarar Bola Tinubu da Femi Fani-Kayode a Amurka.

Dr. Karl Von Batten ya yi zargin cewa tsohon ministan tarayya, Fani-Kayode ya yi masa barazanar sace shi kuma ya yi masa lahani.

Tsohon jigon na PDP wanda yanzu yana tare da Tinubu ya ce bai da niyyar sace kowa ko ya cutar da shi, ya karyata tuhumar da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng