Gwamnonin Arewa 7 Sun Shilla Kasar Amurka, Sun Nemo Abin da Zai Amfani Yan Najeriya
- Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma na neman tallafin ƙasashen waje da jarin ’yan kasuwa domin farfado da yankinsu
- Rahotanni sun nuka cewa jihohi bakwai sun amince da shirin zaman lafiya, tsaro da ci gaba na shekarar 2026 zuwa 2030
- Shirin ya mayar da hankali kan tsaro, samar da ayyukan yi da inganta ayyukan jin daɗin jama’a a yankik Arewa maso Yammacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma na Najeriya na neman tallafin ƙasashen waje da jarin kamfanoni masu zaman kansu domin aiwatar da wani shiri na yankin.
An ruwaito cewa an tsara shirin ne don magance matsalar rashin tsaro, samar da ayyukan yi da inganta ayyukan jin daɗin jama’a.

Source: Facebook
Gwamnatin Jihar Katsina ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, wacce aka wallafa a shafin Facebook.
Gwamnonin sun ganatar da tsarin a Amurka
Ta ce an gabatar da Tsarin Zaman Lafiya, Tsaro da Ci Gaban Arewa maso Yamma na 2026 zuwa 2030 ga hukumomin raya ƙasa da masu zuba jari a birnin New York na Amurka yayin wani taro da aka gudanar a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.
Jihohi bakwai, wato Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara, sun amince da tsarin a watan Maris na 2026.
A cewar Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), taron na New York ya mayar da hankali kan neman haɗin gwiwa da kuɗaɗen gudanar da shirin.
UNDP ta ce an samar da tsarin ne da tallafin fasaha daga gare ta da kuma kuɗaɗen gwamnatin Jamus ta hannun shirin North-west Prevention Facility Project.
Hukumar ta ce an tsara shirin ne domin samar da ayyukan da za su iya jawo kuɗaɗen gwamnati, tallafin hukumomin raya ƙasa da jarin kamfanoni masu zaman kansu.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Fannonin da aka ba fifiko sun haɗa da noma da kiwo, makamash, kayayyakin more rayuwa na kasuwanci, fasaha da ayyukan jin daɗin jama’a.
Shugaban gwamnonin ya gabatar da jawabi
Gwamnan Katsina, Dikko Radda, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, ya ce kowace jiha ita kaɗai ba za ta iya magance matsalolin tsaron yankin yadda ya kamata ba.
A cewar sanarwar da kakakinsa, Ibrahim Mohammed, ya fitar, gwamnan ya ce dole ne a haɗa ayyukan tsaro da matakan magance talauci, rashin aikin yi da matsalar raba mutane da muhallansu.

Source: Facebook
“Dole tsaro ya kasance tare da damar samun ci gaba. Dole tabbatar da zaman lafiya ya kasance tare da ci gaba. Haka kuma, saka hannun jarin gwamnati ya kamata ya samar da damar da jarin kamfanoni masu zaman kansu zai iya shiga cikin harkar ta hanyar da ta dace,” inji Radda.
Ya buƙaci hukumomin raya ƙasa su haɗa tallafinsu a tsakanin jihohi bakwai, sannan ya yi kira ga cibiyoyin kuɗi da ’yan kasuwa su zuba jari a yankinan da ba sa samun isasshen kulawa.
Gwamnan ya kuma ce jihohin na buƙatar inganta haɗin gwiwa, ƙarfafa hukumomi da kuma samar da hanyoyin tabbatar da riƙon amana wajen aiwatar da shirin.
An karrama Gwamna Dikko Radda
Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta karrama gwwmnan jihar Katsina, Dikko Radda saboda kokarin da yake yi wajen tallafa wa mata a jiharsa.
An bai wa gwamnan lambar yabon ne a wajen taron majalisar kasa kan harkokin mata, ci gaban yara da bunkasar al’umma karo na 26, wanda aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba.
Asali: Legit.ng

