Tsohon minista ya sayo wa Tinubu matsala, za a yi karar shugaban Najeriya a Amurka
- Kamfanin Von Batten-Montague-York, L.C ya shirya tsaf zai yi karar Femi Fani-Kayode a kasar Amurka
- Za a kai jakadan mai jiran gado kotu a Amurka saboda zargin ya yi barazanar garkuwa da Karl Von Batten
- Cikin wadanda za su kare kansu a kotun mai zama a Columbia har da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
America - Von Batten-Montague-York, L.C ya ce an ba shi damar shigar da ƙarar dala miliyan 36 a kotun tarayya ta Amurka kan Cif Femi Fani-Kayode.
Von Batten-Montague-York, wani kamfanin hulɗa da gwamnati ne da ke Amurka wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya ɗauka aiki.

Source: Facebook
Von Batten-Montague-York, L.C zai yi karar su Tinubu
A shafin X, kamfanin ya ce ƙarar ta samo asali ne daga zargin barazanar sace shugaban kamfanin, Karl Von Batten, da kuma yi masa lahani da aka yi.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Laraba, ya ce za a shigar da ƙarar a mako mai zuwa a wata kotun tarayya da ke Washington, D.C a Amurka.
Bayanai sun ce an ambaci Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ake ƙara kuma zai kare kan shi.
Rigimar Fani-Kayode da kamfanin Von Batten-Montague-York
Kamfanin ya zargi Fani-Kayode da yin barazanar sace Von Batten tare da cutar da shi a wani shiri da ya ce ya shafi wasu mutane a gwamnatin Najeriya.
Kamfanin ya kuma ce bayan shigar da ƙarar, zai tuntubi hukumomin shige da fice na Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai domin su duba zargin barazanar.
An ji cewa za a sake nazarin izinin Fani-Kayode na yin tafiye-tafiye ko samun bizar shiga waɗannan ƙasashe.
Matakin na zuwa ne bayan jerin saƙonnin da Fani-Kayode ya wallafa a shafinsa na X, ya soki Von Batten kan zarge-zargen da yake ci gaba da yi wa Tinubu.
A makonnin baya-bayan nan, kamfanin Von Batten ya mayar da hankali wajen binciken wasu abubuwan da suka shafi tarihin mu'amalar Tinubu a Amurka.
Kamfanin ya shigar da buƙatun neman bayanai a ƙarƙashin dokar FOI tare da kai wasu ƙara domin samun bayanan Amurka da suka shafi shugaban ƙasar.
Adawar tsohon ministan da kamfanin Amurkan
Tun daga lokacin, Von Batten ya ƙara tsananta sukar da yake yi wa Tinubu, wanda ke neman sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a takarar da za a yi a badi.
Fani-Kayode ya ƙalubalanci Von Batten da ya gabatar da hujjojin zarge-zargensa, tare da yin tambayoyi kan asalinsa, cancantarsa ta aiki da sauransu.
Amma Ambasadan mai jiran gado ya musanta cewa ya taɓa yi wa Von Batten barazanar cutar da shi.
Fani-Kayode ya ce babu wani mai sha'awar kashe ko sace Von Batten, ya ce sai dai yana fallasa mutanen da yake zargi da ƙarya da yaudarar jama'a.
Ya kuma ce yana aiki ne bisa doka kuma zai ci gaba da tunkarar Von Batten ta duk hanyoyin da doka ta ba shi dama.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Asali: Legit.ng

