Trump Ya ba Mutumin Atiku Mukami a Gwamnatin Amurka ana Shirin Zaben 2027

Trump Ya ba Mutumin Atiku Mukami a Gwamnatin Amurka ana Shirin Zaben 2027

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya nada Karl Von Batten, wani ɗan asalin Najeriya kuma mai fafutukar siyasa mukami
  • Von Batten, wanda ke da alaƙa da tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya taɓa yi masa aikin bincike a Amurka a baya
  • Kamfanin Von Batten-Montague-York ya bayyana nadin a matsayin babban abin alfahari, amma bai bayyana takamaiman hukumar da aka nada shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka – Shugaban Amurka Donald Trump ya nada Karl-Marx Edward Ikemefuna William George Okeke-Von Batten mukami.

Majiyoyi suka ce mutumin wanda aka fi sani da Karl Von Batten an nada shi a matsayin kwamishina a wata hukuma a fadar White House.

Trump ya ba mutumin Atiku mukami
Atiku Abubakar da mutuminsa, Von Batten tare da Donald Trump. Hoto: @batten_von, @atiku.
Source: Twitter

Kamfanin Von Batten-Montague-York, L.C., wani kamfanin Amurka mai ba da shawarwari kan manufofi da fafutukar siyasa, ya sanar da nadin a shafin X.

Kara karanta wannan

An samu abin da ya bambanta Tinubu, Atiku da Peter Obi gabanin zaben 2027

An nada Von Batten a ranar Laraba, 2 ga Satumba, 2026, domin ya yi aiki a wata hukumar shugaban ƙasa da ke ƙarƙashin fadar White House.

Trump ya nada Karl Von Batten

Von Batten, wanda aka haifa a Najeriya, ya shahara a fagen siyasar Najeriya saboda alaƙarsa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

A baya, Von Batten ya yi aikin lobbyn Atiku a Amurka, inda yake ƙoƙarin tallata manufofinsa da muradunsa a fagen siyasar ƙasar.

A cikin sanarwar nadin, kamfanin Von Batten-Montague-York ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba ga kamfanin da kuma Von Batten da kansa.

Kamfanin ya ce:

“Von Batten-Montague-York, L.C. na alfaharin sanar da cewa Shugaba Donald J. Trump ya nada Abokin Gudanarwarmu, Dr. Karl Von Batten, domin ya yi wa Amurka hidima a matsayin Kwamishina a wata hukumar shugaban ƙasa ta White House.”
Mutumin Atiku ya samu mukami a gwamnatin Trump
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Kamfanin ya ƙara da cewa: “Dr. Von Batten na matuƙar godiya ga Shugaba Trump (The Chief) bisa wannan naɗi da kuma amincewar da ya nuna masa.”

Kara karanta wannan

Wasikar da Amurka ta aiko Najeriya ta bayyana ainihin shekarun Tinubu a duniya

“Wannan naɗin da shugaban ƙasa ya yi na wakiltar babban abin alfahari ne, kuma yana nuna dogon lokaci da Dr. Von Batten ya sadaukar wajen hidimar jama’a, jagoranci da ƙasarmu.”

“Dr. Von Batten na fatan amsa kiran yin hidima ga shugaban ƙasarmu da kuma Amurka.”

Kamfanin ya ƙara cewa: “Muna taya Dr. Von Batten murnar wannan gagarumin matsayi, tare da yi masa fatan samun nasara a wannan muhimmin aikin hidimar jama’a.”

Wane ne Karl Von Batten?

Von Batten shi ne abokin gudanarwa na Von Batten-Montague-York, L.C., kamfanin da ke bayyana kansa a matsayin mai ba da shawarwari kan manufofi da fafutukar siyasa a Amurka.

A baya, ayyukansa na ba bayanai da suka shafi Atiku Abubakar sun sanya shi cikin mutanen da suka ja hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya.

Sai dai kamfanin bai bayyana takamaiman hukumar shugaban ƙasa da ke ƙarƙashin White House da Trump ya nada Von Batten a cikinta ba.

Atiku ya caccaki FBI kan zargin Tinubu

An ji cewa Atiku Abubakar ya ce bai kamata FBI ta yi amfani da “barazana ga rayuka” a matsayin dalilin boye bayanan da doka ta ba da damar bayyana wa jama’a ba.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da ya shafi abinci, magunguna da sauran bukatun yau da kullum saboda haka kawai bukatar a yi masu bayani.

'Dan takarar shugaban kasar Najeriya a inuwar ADC ya ce kare jami’an FBI da majiyoyinsu ba yana nufin kare gaskiya daga ‘yan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.