Hukumar ICPC Ta Yi Magana, Ta Bayyana Manyan Dalilan Kama Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus
- Hukumar ICPC ta tabbatar da kama tsohon Minista, Geoffrey Uche Nnaji kan zargin gabatar da takardun karatu da na NYSC na bogi
- Hukumar ta ce an kama shi ne bayan ya ƙi amsa gayyatar bincike da aka aika masa ta hanyoyi daban-daban
- Babbar Kotun Tarayya ta ba ICPC umarnin kama tsohon ministan, wanda ya yi murbus akwanakin baya, domin ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta bayyana cewa akwai manyan dalilai guda biyu da suka sa ta tsare tsohon Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Hon. Geoffrey Uchechukwu Nnaji.
Ta ce ta dauki matakin ne bayan tsohon ministan ya gaza amsa gayyatar bincike da aka aika masa a wata takarda mai lamba ICPC/HC/CSTF/GUN/GBT/T.1/VOLV16, ranar 15 ga Mayun 2026.

Source: Twitter
Mai magana da yawun ICPC, John Odey, ne ya bayyana hakan jim kadan bayan bullar labarin kama Nnaji yau Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dalilan ICPC na kama Uche Nnaji
Ya ce bayan Nnaji ya ki amsa gayyatar hukumar, ICPC ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ta samu umarnin kama shi a karkashin ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1160/2026.
Hukumar ta ce an kama tsohon ministan ne a ranar Laraba, 1 ga Yulin 2026, a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan isowarsa birnin.
A cewarta, jami'an Hukumar Tsaro ta DSS sun taimaka wajen cafke shi kafin daga bisani aka mika shi ga ICPC domin ci gaba da bincike.
Ana binciken Nnaji kan takardun bogi
ICPC ta bayyana cewa ana binciken Nnaji ne kan zargin gabatar da takardun bogi guda biyu yayin tantance shi a matsayin minista a shekarar 2023.
Zarge-zargen sun hada da:
- Takardar shaidar digiri daga Jami'ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) da ake zargin ta bogi ce.
- Takardar shaidar kammala bautar kasa (NYSC) da ake zargin ba ta inganta ba.
Yadda Nnaji ya ki amsar gayyatar ICPC
Hukumar ICPC ta ce tun farko ta aika wa tsohon ministan gayyata ta hanyar adireshinsa na Abuja da Enugu, sannan ta kuma tura masa ta hanyar adireshin imel dinsa.
Sai dai duk da wadannan matakai, Nnaji bai halarci zaman binciken da aka tsara ba.

Source: Twitter
Hukumar ta tabbatar da cewa an tsare tsohon ministan a hedikwatarta da ke Abuja, inda za a ci gaba da gudanar da bincike, kamar yadda Premium Times.
ICPC ta kuma tabbatar wa jama'a cewa za ta bi wannan shari'a cikin gaskiya da bin doka har zuwa karshe.
Uche Nnaji ya daukaka ƙara
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya ɗaukaka ƙara kan umarnin kotu da ya ba ICPC damar kama shi bisa zargin jabun takardu.
Baya ga umarnin kama shi, kotun ta kuma bai wa ICPC damar ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ta hanyar jaridu, kafafen sada zumunta da sauran shafukan yada labarai.
Nnaji ya daukaka kara a ranar 18 ga Yuni, 2026 kwanaki biyar bayan ya musanta cewa akwai wani umarnin kotu da aka bayar domin kama shi.
Asali: Legit.ng


